Sunday 4 August 2019

Karanta Addu’a Yayin Kiran Sallah

Tura Wannan Zuwa Ga
Wanda ya ji kiran sallah zai fadi dukkan abin da ladanin yake fadi.

Addu'a Bayan Idar da Sallah


Sai dai idan yace;

حَيَّ عَلَى الصَّلاَةِ، حَيَّ عَلَى الْفَلاَحِ.

Hayya Alas Salah, Hayya Alal Falah.

Ku taho ga Sallah, ku taho ga babban rabo.

Maimakon haka sai shi ya ce:

لا حَـوْلَ وَلا قُـوَّةَ إِلاّ بِالله.

La hawla wala kuwwata illa billah.

Babu daraba, babu karfi sai da Allah.

وَأَنا أَشْـهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْـدَهُ لاَ شَـريكَ لَـهُ، وَأَنَّ محَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسُـولُهُ ، رَضِيـتُ بِاللهِ رَبَّاً ، وَبِمُحَمَّـدٍ رَسُـولاً وَبِالإِسْلامِ دِينًا .

Wa-ana ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-anna Muhammadan AAabduhu warasooluh, radeetu billahi rabban wabimuhammadin rasoolan wabil-islami deena.

Ni ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Kuma Allah shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shi ne Manzo, kuma Musulunci shi ne addini.

Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Sannan ya ce:

اللّهُـمَّ رَبَّ هَذِهِ الدّعْـوَةِ التّـامَّةِ وَالصّلاةِ القَـائِمَة آتِ محَـمَّداً الوَسيـلةَ وَالْفَضـيلَة وَابْعَـثْهُ مَقـامًـا مَحْـمُوداً الَّذِي وَعَـدْتَهُ إِنَّـكَ لا تُـخْلِفُ الْمِيـعَادَ.

 Allahumma rabba hathihid-da'watit-tammah, wassalatil-ka-imah ati Muhammadan alwaseelata wal-fadeelah, waba'ath-hu makaman mahmoodan allazee wa'adtahu, innaka la tukhliful-mee'ad.

Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita. Ka ba wa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma ka tashe mu a matsayi abin godewa, wannan wanda Ka yi masa alkawarinsa. Lallai kai ba ka saba alkawari.

Sannan ya yiwa kansa addu'a tsakanin kiran sallah da tayar da ikama, domin addu'a a wannan lokaci ba a kin karbarta.

ADDU'O"I MASU ALAKA:

Karanta Addu'ar Fita Daga Masallaci

Karanta Addu’a Yayin Cire Tufafi

Karanta Zikiri Bayan Gama Alwala


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user