Monday 24 February 2020

Ka Kasance Mai Tunawa da Wannan a Tsawon Rayuwar Ka

Tura Wannan Zuwa
Idan kana tuna lokacin da kake jariri, wato lokacin da baka iya komai sai dai ayi maka, dole ka ƙara godewa Allah, Allah Shine mai iko.

Rayuwa Tana Faruwa Wucewa Take..

MarubuciSheikh Aliyu Sa'id Gamawa

Idan ka dubi yadda kake a yanzu, wato ka girma har kana iya yiwa kan ka abubuwa da yawa, Tilas kace Alhamdulillahi.

Idan Allah yayi maka tsawon rai, zaka iso zangon da wata rana zaka  tsufa, ka koma komai sai dai ayi maka. Daga nan sai tuba da natsuwa da cewa Allah yasa muyi kyakkyawan ƙarshe.

Kada ka manta da tunanin barin duniya, ranar da za'a rabu da iyalai da dukiya da kome-da kome! Kai tabbas mutuwa wa'azi ce.

Ana son kana tuna cewa wata rana zaka zama gawa, yadda dangi da masoya zasu ɗauke ka su fitar da kai  daga cikin gidan ka! Allah sarki duniya, haƙiƙa rayuwar nan bata da tabbas.

Ɗan uwa wallahi Ni da kai wata rana za'a saka mu a cikin wani rami, a ƙarƙashin ƙasa a ɗora itace a rufe da ƙasa, ba komi ciki sai matsi da duhu gashi ciki babu shimfiɗa! Ba abinda zai baka sauƙi a kabari sai ayyukan da kayi na bin Allah a Duniya. Kai ɗan adam ba komai bane.

Tabbas ba makawa wata rana za a tashe mu daga kabari, a koramu filin hisabi anan ne zamu amsa tambayoyi kan yadda muka gudanar da rayuwar mu. Kai 'yan uwa akwai aiki a gaban mu.

A lahira za a tsayar da kowa domin yayi bayanin abun da ya aikata a duniya! 'Yan uwa mu faɗaka muna yiwa kanmu hisabi kafin ranar hisabin mu.

Bayan hisabi sai shiga wuta ko Aljannah.

Allah ka bamu dacewa da shiga Aljannah kayi mana tsari daga Wuta.

Haƙiƙa ba mai tabbaci na shiga cikin Aljannah! Sai nace mu nace da roƙon Allah yayi mana Rahama.

Dan Allah, mu na tunawa da cewa mutum mai rauni ne.

Allah ya zama gatan mu, Allah Kasa mu dace duniya da lahira Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user