Friday 20 March 2020

Shin Ko Kasan Dalilin da Yasa Mutane Suka Tsane Ka?

Tura Wannan Zuwa
Abokina ya ce min, yayin da wani ya gifta ta kusa da mu:

"Na rasa me ya sa wancan ya tsane ni!"

Sai ya ji na yi shiru.

A Cikin Baƙin Ciki Zasu Dawwama

Marubuci: Hamza Dawaki

Ya ƙara cewa:

"Wai me ya sa mutane haka kawai ba ka yi musu komai ba sai su tsane ka?"

Sai na ce:

"In gaya ma maganar da za ta yi ma daɗi yanzu, ko kuma wadda za ta amfane ka tsawon rayuwa?"

Ya ce:

"A, gaya min wadda za ta amfane nin dai."

Na ce:

"Yayin da wani mutum ya tsane ka, wannan ba matsalarka ba ce. Shi da ya tsane kan, matsalarsa ce, ya je ya yi tunanin don me ya tsane ka. Amma ba kai ba. Za ta iya zama matsalarka ne yayin da ka ji kai ne ka tsane shi. Domin a lokacin ne bincike da tunanin dalilan da suka sa ka tsane shin ya kama ka."

Ya yi dam, har na fara tunanin lallai idan ya kara buɗe baki cewa zai yi bai fahimce ni ba. Amma da zai kara magana sai ya ce:

"Ko me ya sa haka?"

Ni ma na tambaye shi:

"Ko ka san irin azabar da zuciyar wanda ya tsani mutune take sha?"

Ya girgiza kai a sannu game da cewa:

 "A'a."

Na ce mar:

"Yayin da wanda ya tsani mutum yake ɗaukar kaso mai tsoka na dare yana tuno wanda ya tsana ɗin yana baƙin ciki, shi wanda aka tsana wataƙila bai ma san inda kansa yake ba, cikin daddaɗan banci da munsharinsa!"

Sai ya gyaɗa kai, a wannan karon ba tare da magana ba.

Na ƙara tambayarsa:

"In gaya ma ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suke haddasa saurin tsufa da manyan cutuka?"

Ya ce: "Eh." cikin sauri.

Na ce mar:

"KWANCIYA DA BAƘIN CIKI!".

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user