Thursday 9 April 2020

Mace Mafi Daraja A Duniya

Tura Wannan Zuwa Ga
An tambayi wani mai hikima dangane da mace.

Mace Mafi Daraja A Duniya...

Marubuci:- Abu Unaisa

Sai ya bada amsa:

Idan mace ma'abociyar Addini ce to tana da daraja =1.

Idan ta zama mai Kyau sai a ƙara sifili (0) akai ta zama tana da daraja =10.

Idan tazama mai Dukiya sai aƙara mata sifili (0) ta zama tana da daraja =100.

Idan ta zama mai Nasaba sai aƙara mata sifiri (0) ta zama tana da daraja =1000.

Amma idan tara sa guda ɗayan farko wato addini sai a cire ɗaya (1) sai ya zama ba abin da ya ragu sai sifilai = 000.

Dan haka bata da komai na ƙima da daraja ta rasa duk wani abu da zai mata ado da gata a duniya da lahira.

Ki yi ado da Addini da Ɗabi'a, idan kika rasa su kin zama fanko ba abin da yayi saura.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user