Friday 3 April 2020

SHARRIN DARE DA RANA

Tura Wannan Zuwa Ga
MAFI ALKHAIRI A DUNIYA DA LAHIRA

Ka nemi tsari daga sharrin dare da rana, kada kai tunanin ai kai babu wanda zai nufe ka da sharri komai ƙanƙantar sa idan ka yarda da wannan tabbas kana yaudarar kanka ne, domin koda kuwa kai ba kowa bane to akwai wanda bayason Ci gaban ka ko kuma baya son ganin Ka a raye, saboda babu yadda zai yi shiyasa zai biyo maka ta bayan gida, wataƙila ma na kusa dakai ne, shiyasa Allah Maɗaukakin Sarki bai saukar da cuta ba sai da ya fara saukar da maganinta , sai dai idan ba a sani ba.

NEMI TSARI

Ka yarda da cewa "Allah ne kaɗai zai iya baka sannan kuma ya karɓa a lokacin da yaso". Kada ka taɓa zargin wani (Bawan Allah) da hanaka abinda Allah bai baka ba, dama can ba rabon ka bane.

Roƙi Allah zaɓi mafi alkhairi sai kaga ka dace anan Duniya da kuma Lahira.

Allah ka tsare Mu da Tsarewar Ka daga dukkan sharri na zahiri da kuma na ɓoye Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user