Saturday 18 July 2020

Shin Ko Kasan Bambancin Yaran Zamani Da Yaran Da Suka Rayu A Zamanin Iyaye Da Kakanni?

Tura Wannan Zuwa Ga
A haƙiƙanin gaskiya yaran mu na wannan zamanin sun sha bamban da zamanonin da suka gabata musamman yanayin saurin girma da kuma wayo da fahimtar abubuwa da wuri wajen lura da kuma koyo.

YARA MANYAN GOBE !!!

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Ya kamata iyaye su sanya ido a rayuwar 'ya'yansu musamman wajen basu ingantacciyar tarbiyya da jajircewa  wajen ganin sun taso da kyakykyawar ɗabi'a da nagartaccen ilimi ta fannin addini da na zamani.

Me ya kamata iyaye suyi a dai-dai irin wannan lokaci da yaransu suke ƙoƙarin kwaikoyon abubuwa da dama?

A dai-dai wannan lokacin ne ya kamata iyaye su fara kai komo wajen cusawa yaransu tarbiyyah nagari, hakanan su ɗin ma ya dace su zamanto nagari, domin a dai-dai wannan lokacin ne yaran zasu zamto (Photocopy) na iyayensu ma'ana zasu ringa kwaikwayon ɗabi'un iyayensu mai kyau da maras kyau.

Kada kice: "Yarinyata bata isa sanya hijabi ba ". A'a fara sanya mata tun  daga wannan lokacin, Kada kice "Yarona bai isa zuwa masallaci ba". A'a yi masa alwala ki haɗa shi da mahaifinsa ki lallaɓa shi ta hanyar jan hankali da hikima cewa idan yaje kada yayi fitsari to sai kiga yaro sunje sun dawo ba tare da yayi fitsari a masallaci ba.

Domin iccenka tun yana ɗanye ya kamata ka tanƙora shi domin idan ya riƙa ya bushe bazai tanƙora ba.

Idan ALLAH yabawa yaro lafiya da wayo yana da shekara huɗu zuwa biyar ko shida maganarsa zata kasance ana ganeta sosai, a dai-dai wannan lokacin malamarsa (Mahaifiya) zata fara koya masa muhimman abubuwa kamar: sallama idan zai shiga gida ko ɗaki, gaida mutane, tsarki, alwala, karatun alƙur'an mai girma, idan mace ce a ringa yawan sanya mata hijab da dai sauransu.

Sallah kuma a dai-dai wannan lokacin zata dinga umurtarsa yana kwaikwayonta, idan ya kai shekara bakwai sai ta koya masa abunda ake faɗa a iƙamah da kabbara da tsayuwa da ruku'i da sujjada da tahiya da dai sauransu.

Yazo a Hadith cewa: A umurci yara suyi sallah tun daga shekara bakwai, a dake su idan sunƙi yin sallah suna da shekara goma.

Ba lallai bane iyaye su zauna har sai yaransu sun kai shekara bakwai sannan su fara musu umurni da Sallah, A'a idan kuka fahimci yaranku suna da saurin fahimtar abubuwa da ganewa za'a iya fara musu umurni da yin sallah tun kafin shekara bakwai.

A gaskiya akwai ƙalubale ga iyaye ko ma nace ga al'ummah, yaro ƙarami mai shekara huɗu zuwa biyar idan ya furta maka wata maganar sai ka rasa inda zaka sanya kanka.

Abun takaici sai kaga yaro ƙarami yasan sunayen 'yan fim ya kuma haddace tsaf, amma bai san sunayen ALLAH ba, yasan waƙoƙi har yana rera su amma bai san abyaat na addini ba !!! Koda yake wannan ƙalubalen bai tsaya ga yara kaɗai ba domin sai ka samu babba yasan sunayen 'yan fim da na 'yan wasan ƙwallon ƙafa zai iya kawo maka su daka amma bazai iya kawo maka sunayen ALLAH guda goma ba. Ya kamata muji tsoron ALLAH mu ringa fifita addini sama da komai.

Babbar kyautar da iyaye zasu yiwa 'ya'yansu shine su samar musu da ingantacciyar tarbiyya musamman a yadda muka tsinci kanmu a wannan zamanin na taɓarɓarewar tarbiyya da lalacewarta ga al'ummah, asalin tubalin da zaka fara gina ingantacciyar tarbiyya ga 'ya'yanka shine ka sama musu Nagartacciyar Uwa Tagari wacce ta cancanci ta zama madubi abun koyi ga al'ummah.

Duk runtsi duk wahala kuyi ƙoƙarin ganin yaranku sun taso da kyakykyawar tarbiyya da ilimin addini da na zamani da sauke dukkan abunda Musulunci ya ɗaura muku dangane dasu, idan kuka yi haka kun fita haƙƙinsu.

Kada ku manta acikin Alƙur'ani mai girma ALLAH (S.W.T) Yace:


يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا قُوا أَنفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ ...

Ma'ana: "Yaku waɗanda kuka yi imani! Ku kare kanku da iyalanku (daga) wata wuta makamashinta mutane da duwatsu... [Tahrim:06]

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: "dukkan ku masu kiwo ne kuma kowa za'a tambaye shi akan abin kiwonsa."

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user