Friday 4 September 2020

Karanta Hirar Masoyan Asali

Tura Wannan Zuwa Ga
KE KYAKKYAWA CE MASOYIYA TA

Tabbas Furanni suna da ƙamshi, Zuma kuma tana da zaƙi launin ciyawa kuma kore ne, amma ke babu wata kalma da zata iya bayyanar da zahirin siffarki sai dai kawai na ce ke kyakkyawa ce. Ina son Ki.

Hirar Masoya

MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa

KAI NAKE SON GANI A KODA YAUSHE

Masoyina ko ka san cewa cikin kowace rana kyawunka daɗuwa yake yi a cikin idanuwana? Tabbas ba zan dakata daga begen kallon kyakkyawar surarka a zahiri da kuma cikin zuciyata ba har sai gobe hasken idaniyata, hmm! karda ka manta a goben ma sai gobe. Ina son Ka.

IDAN KIKA RABU DA NI ZAN SHIGA  HAƊARI

Son ki a cikin zuciyata tamkar numfashi ne da yake futa daga hancina wanda tsayar da shi dai-dai yake da mutuwata, idan haka ne tayaya kike ganin zan iya futar da son ki daga cikin zuciyata? Ina son Ki ma'abociyar kyawu. Ki huta Lafiya

NI TAKA CE HAR ABADA

Farin ciki mara misaltuwa kan ziyarci zuciyata a dukkan lokacin da na ji sautin muryarka, murmushinka babban abu ne da yake yayen damuwa, bana kasancewa dai-dai da shaƙar numfashi ba tare da tinaninka ba a cikin zuciyata, kaine ɗaya tilo da na damƙawa ragamar zuciyata. Ni taka ce har abada, Ina son ka

BA ZAN TAƁA MANTAWA DA KE BA A RAYUWA TA

Samuwar ki a cikin rayuwata ya samar da gagarumin canji ga ƙaruwar farin ciki na ta hanyar sauraren muryarki da kuma kasantuwata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsari. Duk wani abu da zan furta yau a gare ki ba zai wuce, ina Son ki ba, ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, sannan kuma kina ɗaya daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da su ba har abada a rayuwata. Ki huta Lafiya.

HM! MASOYINA SARKIN ADO

Da akwai watarana da na tanada domin nishaɗantuwa da kallon tattausan murmushi daga wata kyakkyawar fuska ta wani kyakkyawan saurayi gwanin iya ado, ba kowa bane face kai annurin raina shin ko zan samu gani ko jin murmushin ka cikin wannan rana masoyina? Ka huta Lafiya

RAYUWAR MU NA TAFIYA IRI GUDA GANGAR JIKIN MU CE TA BANBANTA

Kasantuwar mu raye cikin ruhi guda ɗaya ya sanya zuciyoyin mu bugawa cikin lokuta makamanta juna. Komai na mu ya kasance yana faruwa ne a lokaci guda hatta baƙin ciki da kuma farin ciki, wato ruhi guda gangar jiki kuma biyu. Farin cikin ki shi ne nawa, ina son ki. Barka da kasancewa cikin wannan rana masoyiya Ta.

BURINA MU KASANCE CIKIN INUWA ƊAYA MASOYINA

A cikin kowace safiya na kan tashi cikin farin ciki saboda ina sanya ran a ko da wane lokaci zan iya ganin ka amma zuwan dare kan yi sanadiyar zubar hawaye daga idaniyata saboda lokaci ne da yake nisanta tinanina ga tsammanin sake ganin ka a koda wane lokaci kafin wayewar gari. Fatana ka fahimci cewa ina son ka ina kuma shiga damuwa a lokacin da na nesanta da kai. Ina ƙaunar ka masoyi Na.

FATANA BAI WUCE

Ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciyata. Fatana a kullum ki gamsu da cewa, Ina Son Ki

MUNA NAN TARE CIKIN DARE KO RANA MASOYINA

Shin masoyina izuwa yanzu ko ka fara jin gajiya a jikinka kuwa? Saboda ka kasance kana motsi a cikin zuciyata a tsawon dare ka kuma kasance mai zagaya dukkan jikina ta kafar da jinin jikina ne kawai yake gudana a cikin kowace safiya da yini. Ina son Ka

KARDA KI NESANCE NI INA TARE DA KE

Ko da ya kasance kin nesanta da ni, ni kuma zan kasance a tare da ke har abada, bakina kan gaza furta kowace irin kalma domin bayyana miki adadin yadda nake son ki a dukkan lokacin da muke tare amma cikin dare ko safiya zuciyata na bayyana min cewa, ke ce farin cikina, fitila mai kore duhun zuciyata, Zara kike tauraruwa cikin taurari. Ina son Ki. Ki huta Lafiya

INA SON BAYYANA MIKI CEWA 

So tamkar hasken rana yake da yake haske fuskar da take ɗauke a jikin gangar jiki ma'abociyar zuciyar da take ƙunshe da So. Kasantuwar SO a cikin zuciya kan motsa ruhi ya kuma busar da idanuwa daga barin yin bacci a mafi yawancin dare, So kan samar da wasu rassa a cikin zuciya bayan bayyanar sa, wato baƙin ciki da kuma farin ciki. Zan ci gaba da son ki a cikin kowane irin yanayi. Ina Son Ki

MU KASANCE TARE HAR ABADA.

Masoyiyata ina neman alfarmar da ki mallaka min zuciyar ki, na daɗe da mallaka miki tawa lokuta masu yawa da suka shuɗe abokai ma shaida ne, bayan ya kasance kin mallaka min ita ni kuma zan haɗa su na ɗaure su waje guda da sarƙar soyayya mai ƙarfi na jefa makullin a cikin tekun maliya. Ki amince ina son ki wannan shi ne burina. Ki huta Lafiya

SAMUN KI A RAYUWATA BABBAR NASARA CE

Matata Uwar 'ya'yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki ɗaya, ina cike da zumuɗin son dawowa domin cin girkin ki mai daɗi. ki kula min da kan ki, sai na dawo. Ina son ki mata Ta

KO KIN SAN YAYA NAKE JI IDAN BANA TARE DA KE MATATA?

Nesantar ki babban aiki ne da yake jigata zuciyata, dama ace zaki iya fuskantar halin matsi da takura da nake shiga da kuma shauƙin Son kasancewa a tare da ke da nake ji cikin zuciyata a dukkan lokacin da na nesanta da gida. Ina fatan zaki ci gaba da kula min da kan ki har zuwa lokacin da zan dawo gida. Allah ya tsare min ke matata, ina son Ki

SAKO MAI MUHIMMANCI

Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin ka/ki a ko'ina wato Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user