Saturday 31 October 2020

Rarara Yace Duk Wanda Baya Son SARS Ba Dan Kishin Cigaban Nigeria Bane

Tura Wannan Zuwa Ga

A cikin wata gajeriyar tattaunawa da ayi da fitaccen mawaƙin siyasar ƙasar Nijeriya Dauda Kahutu Rarara yace "Duk wanda kaji yace baya ƙaunar SARS, to bawai baya ƙaunar SARS bane, baya ƙaunar Nijeriya ne". 

Dauda Kahutu Rarara

Saboda rundunar SARS tana ƙoƙarin a gyara Nijeriya ne da al'ummar cikin ta, musamman waɗanda suke cin hanci da rashawa.


Ya ƙara da cewa "Bazaka san amfanin Nijeriya ba, har sai kaje cikin wata ƙasar daban ba Nijeriya ba".


Daga ƙarshe yayi kira ga shahararrun mawaƙa da 'yam fim da cewar kowannen su, yana da tashi rawar dazai taka wajen ginuwar al'ummar ƙasar Nijeriya.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user