Monday 28 December 2020

KARANTA ILLOLIN YIN KARYA GA RAYUWAR MUSULMI

Tura Wannan Zuwa Ga

Ya zo a Hadisin da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (R.A) yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: ((Ana iya halittar mumini da kõwace irin ɗabi’a/ta’ãda -marar kyau- in ban da yaudara da kuma ƙarya)). Imãm Ahmad da Baihaƙy.


Nesantar Karya Da Kuma Yaudara


Marubuci: M. Abba Lawan Hassan


Idan bãwa ya ɗabi’antu da ƙarya; to, wannan hanya ce da babu makawa sai ta kai ga mai yin ta cikin wuta, don ƙarya tana kai mutum zuwa ga munãfurci wanda kuma shi ne tushen dukkan munãnan ayyuka.


Bisa ga haka sãɓa alkawari ba wani abu bane fãce yin ƙarya wacce ta ƙunshi faɗin abu da bãki da kuma aiki da gaɓɓai baki ɗaya.


Yin alguss da yaudara ƙarya ne wacce ta shãfi aikin gaɓɓai da kuma shaidar zur, sã’ilin nan ƙarya ga wanda ya riƙe ta a matsayin tushen arziƙinsa; to, lalle ya riƙi babban tushe na sãɓo.


A wannan zãmani ƙarya da yaudara sun gama fantsuwa a tsakãnin mutane abin bai bar shugabannin siyasa da sarauta ba, haka ma ƴan kasuwa da ma’aikata, haka ma dai maza da kuma mãta, Allah ya gyãra mana hãlãyan mu! Allah ya Dãtar Da Mu Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user