Sunday 24 January 2021

Shin Ko Kasan Fuska Biyu Sharri Ce Ga Mai Ita?

Tura Wannan Zuwa

Yana daga cikin manyan musíbun da Allàh Subhànahu wa Ta'àlà Ya jarabi da yawan musulmi , yin fuska biyu a cikin mu'àmalar da suke yaƙan junan su.


Fuska Biyu Sharri Ce Ga Mai Ita


Marubuci: Sheikh Muhammad Kabir Haidare


Babu ko shakka yin haka haràmun ne , domin wata ƙofa ce mutum ya buɗewa kansa ta yaudara , ha'inci , cin amanah da kuma zamba cikin aminci.



Dangane da wannan ne ma Manzon Allàh  صلى الله عليه و على آله و سلم  ya gargaɗi al'ummar sa dangane da wannan.



A cikin Hadíthin da Bukhàrí da Muslim (rahimahumàllàh) suka  ruwaito , Manzon Allàh ( S.A.W) yake cewa : 


" تجدون من شرار الناس ذا الوجهين  ، 

الذى يأتى هؤلاء بوجه و يأتى  هؤلاء بوجه " 


                        ma'ana


" Zaku samu  daga cikin mutane masu sharri , mutum mai fuska biyu. Shine wanda zai je wa waɗannan mutanen da wata fuska ( ta cewa yana tare dasu) , 

sannan kuma sai yaje wa waɗancan da wata fuska kuma ta daban ( cewa yana tare da su) " !

           

              ABUBUWAN LURA 


1. Yin fuska biyu na cutar da ɓangarorin nan biyu dukan su , domin ko wanen su yana ganin cewa wannan mutum nasu ne, saboda ya same su ya nuna cewa yana tare da su a cikin tafiyar su.


Sai bayan da suka saki jiki da shi , sai ta bayyana cewa ga haƙíƙanin sifar sa ! 


2. Yin haka sifah ce ta munafukai masu cewa sun yi ímàni da Allàh da Manzon Sa (S.A.W) , to amma ba musulmi ba ne ba su, kàfirai ne ! 


3. Ba dukan munàfiki yake kàfiri ba , a'a akwai ƙaramin munàfiki wanda shi musulmi ne , munàfincin sa baya fitar da shi daga musulunci amma kuma duk da haka sai ya shiga wuta idan har bai tuba ba ! 


4. Mai fuska biyu ba zai taɓa kuɓuta daga waɗannan hàlayen ba :


(a)____ Ƙarya 

(b)____ Yaudara

(c)____ Cin amanah

(d)____  Saɓa alƙawari

(e)____ Son zuciya

(t)_____ Rashin gaskiya


5. Yin fuska biyu yana zubar da mutunci , kwarjini da ƙímar mutum .


6. Kada mai karatu yayi tsammanin taƙaituwar wannan Hadithin ga wasu mutane banda wasu, a'a kowa na iya shigowa cikin hadarin wannan Hadíthin.


Saboda haka mutumin da Allàh ya kuɓutar da shi wannan hadarin  haƙíƙah ya rabauta duniya da lahira.


7. Babban wurin da wannan ɗabí'ah tafi muni da cutarwa shine a cikin aƙídah , 

kamar mutum ya bayyanar da kansa ahlus Sunnnah sahihi kuma Salafí , amma sai ya kasance yana da wata aƙídah ko inhiràfi ( fanɗarewa) wadda yake tallatawa.


Allàh Ya tsare mana ímànin mu Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user