Thursday 25 February 2021

Kalubalen Dake Gaban Saurayi

Tura Wannan Zuwa Ga

Babban gatan da Ɗa Namiji zai yiwa kansa shine ya mayar da hankali kan neman Kuɗinsa da Ilimin sa, idan so samu ne kar ya bari ɗaya ya hana ɗaya, sai dai idan dole ɗayan zai riƙe ya haƙura da ɗayan ba yadda zai yi.


KALUBALEN NAMIJI (SAURAYI)

MarubuciyaFatima Zahra


Kar ya yarda ya saki sana'ar da take hannunsa ko wani aiki da yake yi wanda yake samun na rufin asirinsa, in har ba wani wanda ya fishi ya samu a hannu ba.


Kar ya dinga hangen wanda ya fishi wani abu ko ya dinga biyewa waɗanda suka fishi yana ƙyamar sana'ar da yake yi wanda kuma itace rufin asirinsa da mutuncinsa.


Kar ya bari saboda mace ya dinga kunya ko jin nauyin neman halak ɗin sa, In za taso shi a haka taso shi, idan baza taso shi ba ya barta taje tayi da abokin burminta, ya zamo mai tattali domin gina gobensa, sannan kar ya zamo marowaci domin akwai albarka cikin kyautatawa, ya kuma yawaita neman albarka da Addu'ar mahaifa.


Shi Namiji yana da hanya shararriya wacce yake buƙatar yin aiki tuƙuru da shirya mata kafin ya fara binta.


Allah ya rufa asiri Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user