Saturday 16 June 2018

SHIN DAGASKE NE JARUMI ALI NUHU YA FITO TAKARAR GWAMNAN JIHAR KANO?

Tura Wannan Zuwa


Fitaccen Jarumin Fina-Finan Hausa Ali Nuhu ya karyata labarin da yake yawo a kafafen sada zumunta Na Yanar Gizo akan Cewa"Ali Nuhu Yafito takara a Jam'iyyar APC mai Mulki a Nigeria a matsayin gwamnan Jihar Kano wacce take tarayyar Arewacin Nigeria ".

Jarumi Ali Nuhu

Sai dai Jarumin tini yafito  shafin sada zumunta da Muhawara Na Internet ya karyata labarin da ake yadawa


Ga cikakken abinda ya Rubuta Kamar Haka:

'Ire-iren wadannan hotunan da suke yawo a shafukan sada zumunta ba gaskiya bane/Kindly disregard such posts fake mnews Kannywood.".


Idan masu karatu baza Ku manta ba muryarhausa24.com.ng a makon da ya gaba ta mun kawo muku Labari akan cewar" Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu, ya ce ba zai taba shiga harkokin siyasa ko tsayawa takara ba, duk kuwa da irin farin jini da daukakar da yake da ita"."

A binciken muryarhausa24.com.ng  akan takaitaccen Tarihin Rayuwar Jarumi Ali Nuhu ga Kadan daga ciki:

An haifi jarumin mai tauraro wanda aka yi ma lakabin sarkin Kannywood » a garin Maiduguri ranar 15 ga watan Maris na shekara 1974.

Yayi karatun kuruciyar sa a jihar Kano kana ya tafi jami'ar Jos daga baya ya ketara zuwa jami'a birnin Carlifonia inda ta karanci ilimin shirya fim.

Jarumin ya fara harkar fim gadagadan cikin 1999 kuma yana taka rawa wajen shiryawa da bada umarni har ma rubutun shiri.


Jarumi Ali Nuhu

Ali Nuhu yana daya daga cikin kusoshin Kannywood da suka raya masana'antar bisa gudunmawar da yake badawa wanda bata da iyyaka.

Dadewar sa tare da nuna basirar shi na wasan kwaikwayo bai tsaya a kan fina-finan hausa kadai, jarumin yana haskawa a cikin fina-finan kudancin kasar ta Nollywood.

Ya samu kyaututuka da dama bisa rawar da yake takawa a bangaren nishadantarwa cikin gida har da kasashen waje.

Jagoran kamfanin FKD yayi sanadiyar fitowar jarumai da dama da ke tashe a masana'antar a halin yanzu.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng


Source: www.muryarhausa24.Com.ng

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user