Monday 17 June 2024

Ku Daina Damuwa Saboda Rashin Karatun Boko

Tura Wannan Zuwa Ga
Wasu mutane sukan raina kansu, sukan ji cewa su ba su da wani kima da daraja tunda ba su yi boko ba.

KADA KU DAMU DON BA KU YI BOKO BA
Hoto: Dreams time


Marubuci:- Kamaluddeen Kmc


Ya kai mai irin wannan tunani, ka sani cewa, boko ba wani abu ba ne illa ka iya karatu da rubutu, idan ka san yadda za ka rubuta abu sannan kuma ka iya karanta abu, da yardar Allah ka more.


Kowa da kiwon da ya karɓe sa. Wasu boko ce sana'ar su. Wasu kuma kasuwanci suka sa a gaba.

Fatan kowa dai samun rufin asiri yake yi.


Ubangiji Allah ya buɗa wa kowa ƙofar arzikin sa, ya kuma albarkaci dukiyoyin mu da kuma rayuwar mu baki ɗaya.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user