Friday 7 June 2024

Karanta Addu'a Ga Mamacin Yaro Yayin Sallar Jana'iza A Gare shi

Tura Wannan Zuwa Ga


اَللَّهُمّ أَعِذْهُ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ.


Allahumma a'izhu min azabil kabr.


Ya Allah! Ka tsirar da shi daga azabar kabari.


Idan kuma ya karanta wannan addu'ar to yana da kyau; an same ta daga cikin littattafan wasu Malamai.


Addu'a Ga Mamacin Yaro Yayin Sallar Jana'iza A Gare shi
Hoto: AMAA Muslim Cemetery 


اَللَّهُمّ اجْعَلْهُ فَرَطاً وَذُخْراً لِوَالِدَيْهِ، وَشَفِيعاً مُجَاباً، اَللَّهُمّ ثَقِّلْ بِهِ مَوَازِينَهُمَا، وَأَعْظِمْ بِهِ أُجُورَهُمَا، وَأَلْحِقْهُ بِصَالِحِ الْمُؤْمِنِينَ، وَاجْعَلْهُ فِي كَفَالَةِ إِبْرَاهِيمَ، وَقِهِ بِرَحْمَتِكَ عَذَابَ الْجَحِيمِ. وَأَبْدِلْهُ دَارًا خَيْرًا مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلاً خَيْرًا مِنْ أَهْلِهِ، اَللَّهُمَّ اغْفِرْ ِلأَسْلاَفِنَا، وَأَفْرَاطَنَا، وَمَنْ سَبَقَنَا بِاْلإِيـمَانِ.


Allahummaj-'alhu faratan, wazukhran liwalidayh, washafee'an mujaban. Allahumma thaqqil bihi mawazeenahuma wa-a'zim bihi ojoorahuma, wa-alhikhu bisalihil-mu'mineen, waj'alhu fee kafalati Ibraheem, wakihi birahmatika 'azabal-jaheem. Wa abdilhu daran khayran min darihi, wa ahlan khayran min ahlihi. Allahumma ghfir li-aslafina wa afratina wa man sabaqana bil iman.


Ya Allah! Ka sanya shi lada abin gabatarwa, abin ajiyewa ga iyayensa, kuma mai ceto wanda ake karbar cetonsa. Ya Allah! Ka nauyaya ma'aunan ayyukansu das hi, Ka girmama ladaddakinsu da shi, kuma Ka riskar das hi da salihan muminai, Ka sanya shi cikin renon Annabi Ibrahim. Ka tserar das hi da rahamarka daga azabar wuta, ka musanya masa gida day a fi gidansa alheri, da iyali da suka fi iyalinsa alheri. Ya Allah! Ka gafarta wa wadanda suka riga mu (gidan gaskiya) da 'ya'yanmu da suka riga mu (gidan gaskiya) da wadanda suka gabace mua cikin imani.


Hasan Al-Basri ya kasance yana karanta fatiha a wajen sallar gawa ga yaron da ya mutu sannan yace; 


اَللَّهُمّ اجْعَلْهُ لَنَا فَرَطاً، وَسَلَفاً وَأَجْراً.


Allahummaj-'alhu lana farata, wasalafan wa-ajra.


Ya Allah! Ka sanya shi magabaci, da marigayi, da lada gare mu.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user