Tuesday 11 June 2024

Zazzafan Sakon Soyayya Daga Masoyiya Zuwa Ga Saurayi

Tura Wannan Zuwa Ga

Amincin Allah ya tabbata a gare ka, haɗe da hamshaƙiyar sassanyar iska wacce take busawa a sararin samaniya mai ɗauke da ƙamshin furanni tare da fatan kana lafiya.


Zuwa ga masoyina
Hoto: Csfhungary


Marubuci: Imran Musa Jahun

Ina so na miƙa gaisuwa tsaftatacciya kuma tabbatacciya zuwa ga mutum ingantacce kamar ka.


Ɗimbin soyayya da aminci da yarda da murna da farin ciki marasa ƙarewa a gare ka namiji ɗaya tamkar dubu, haƙiƙa kai ne wanda na ba wa mulkin zuciyata, kai ne wanda ɓacin ranka ke girgiza ni, kuma kai ne wanda hawayen ka kan zamto tamkar ruwan zafi a gare ni. 


Musamman lokacin da na ji wata wadda kake so ta yi fatali da kai nasan ka sha kuka, hakan yasa zuciyata tamkar garwashi ne a cikinta.


Sannan ina miƙa shimfiɗaɗɗiyar murnata mai ɗauke da dawwamammiyar ƙauna tare da goyon baya a cikin soyayyar mu.


Ya wanda sautin muryar ka take rikitar da ni ta kuma gigita ni saboda tsananin ƙaunarka da nake mai sona.


Ina so na faɗa maka irin ribar da na samu a sakamakon haɗuwa ta da kai.


Bari na dakata anan domin na ga kamar ranka ba ya so, domin ka san na ƙi jinin  ɓacin ranka, zan riƙe ka amana ba zan yada kai ba har abada insha Allah.


Na turo maka saƙon gaisuwa ne kafin mu yi waya, kuma ina mai jaddada maka cewa ina alfahari da kai abin ƙaunata.


Ka huta lafiya.


Taka a kodayaushe...


Na Mazan yana nan tafe.


Shin wacce irin amsa za ka mai dawa masoyiyarka idan ta turo maka irin wannan saƙon?


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user