Tuesday 2 July 2024

Alamomin Tabbatar Da Karewar Soyayya A Tsakanin Ku

Tura Wannan Zuwa Ga

Akwai alamomin da Namiji zai nuna miki waɗanda ko shakka babu ya daina son ki, babu sauran ɓurɓushin soyayyar ki a cikin zuciyar sa, amma soyayyar da kike yi masa ya sa kina kokwanto a kan shi yana sona ko bai sona?


Alamomin Tabbatar Da Karewar Soyayya A Tsakanin Ku
Hoto: Paired life


Marubuciya:- Ummy Bint Abubakar


Waɗannan alamomin za su warware miki matsalar da kike ciki.


Ga su kamar haka;1. Zai yanke duk wani nau'in sadarwa da ke tsakanin ku.


Ma'ana duk wata hanyar da za ta haɗa ku ku yi magana zai datse ta. Misali zai rage zuwa gidan ku fira/hira da sunan zance, wataƙila a sati da yana zuwa sau uku, daga lokacin da ya daina son ki zai koma sau ɗaya har sai kin wayi gari ma a sati ko ƙeyar sa ba za ki gani ba. 


Da kin yi ƙorafi zai nuna miki cewa aiki ne ya yi masa yawa. 


Sannan idan ma'abocin turo da saƙon text messages (SMS) ne nan ma zai rage har sai ya dawo ba ki ganin ko ɗaya. 


Wajen kiran waya kowanne masoya su na da tsarin kiran junansu ta waya, wasu su kan tsara lokutan wayar, daga lokacin da kika fahimci cewa ya daina bin wannan tsarin, kullum ke ce ke kira, bai miki bayanin komai ba to maganar soyayya babu ita.


Har ya zama duk wata magana da ta shafi soyayyar ku ke ce ke yin ta, to ki tabbatar da cewa ya daina son ki ne, saboda soyayya ba ta tafiya ba tare da taimakon kowanne ɓangare ba, dole ne kowane ɓangare ya bada gudummawa.


2. Daga lokacin da ya fara kwatanta ki da wata Mace.


Kowace mace burinta a ce masoyinta bai da wani ido a kan wata 'ya/ɗiya mace face ita. 


Da zaran Namiji ya fara haɗa ki da wata, yana nuna gazawar ki a kan wasu abubuwan, yana nuna me ya sa ba za ki zama kamar wance ba? To ki tabbatar ya fara daina yayinki ko son ki. 


Duk namijin da ke son ki yana ganin kin fi kowacce mace, ko da kuwa a zahiri ba haka ba ne ba ko Bature ya ce "Beauty is in the eyes of beholder". 


Daga lokacin da ya fara ce miki "Me ya sa ba za ki yi koyi da rayuwar Wance ba? Wai ke ba za ki koyi yanayin kwalliya da adon Wance ba? Ina ma a ce za ki iya zama Mace kamar yadda Wance take? Wai ke mai ya sa kin cika kishin tsiya ne? Budurwar Wane ba haka take ba".


Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user