Tuesday 6 August 2024

Asalin Samuwar Shubuhohi A Musulunci

Tura Wannan Zuwa Ga

Shubuhohi suna samun asali ne daga: 


1. Jahilci


2. Son zuciya 


3. Kare bidi'a


4. Yaɗa ɓata


5. Son a karkatar da musulmi daga tafarkin sunna. 


Asalin Shubuhohi A Musulunci
Hoto: Depositphotos


MarubuciAhmad Murtala Mansur


Waɗannan su ne muhimman dalilan da ke haifar da shubuhohi da yaɗawar su a cikin al'umma. 


Yahudu da Nasara da 'yan kanzagin su daga fanɗararrun musulmai masu ƙirƙirar bidi'o'i da yaɗa munanan aƙidu, da munafukai, su ne suke ta fafautukar zaƙulo shubuhohi da ƙera su da yi musu kwalliya tare da yaɗa su. 


Allah Ta'ala ya ce 


يااهل الكتاب لم تلبسون الحق بالباطل وتكتمون الحق وانتم تعلمون


"Ya ku ma'abota littafi me ya sa kuke cuɗanya gaskiya da ƙarya , kuma kuke ɓoye gaskiya alhali kuna sane ? 


Al-Imran : 71. 


Halayen masu yaɗa shubuhohi suna da ban haushi da mamaki ta yadda ƙiriƙiri suke ƙoƙarin ta kowane hali sai sun mayar da baƙin abu ya koma fari, ko kuma su munana fari wai sai ya koma baƙi. 


Ibnul Ƙayyim Rahimahullahu ya ce: 


"Yana daga siffofin munafukai ɓoye gaskiya, da kawo ruɗani ga masu bin gaskiya, da aibata mutane da laifukan da su ne suke aikata su. "


Idan suka ga wasu suna ƙoƙarin hana ɓarna da kawo gyara sai su tsane su, su rinƙa ce musu maɓarnata masu haddasa fitina. Alhali Allah da Manzon sa da dukkannin muminai sun san cewa su ne cikakkun maɓarnata fitinannu.


Idan Malamai magada Annabawa suka kira su zuwa ga littafin Allah da Sunnar Manzon sa sai su rinƙa kiran su da sunan 'yan bidi'a ɓatattu. 


Idan suka gan su ba su damu da abin duniya ba, sai su ce ƙaryar Zuhudu suke yi mayaudara ne. 


Idan suka bayyana gaskiya sai su kawo ƙarerayi su haɗe su da wannan gaskiyar su muzanta wannan gaskiyar a idon jahilai da masu raunin fahimta, don su ruɗa su, su karkatar da su , su hana su fahimta da bin gaskiya. 


Suna ɗauko ƙarya su lulluɓa mata riga ta gaskiya don a yarda da su da wannan ƙaryar ta su. "


(طريق الهجرتين ٦٠٢_٦٠٣)


Wato dai Shubuhohi su ne tushe kuma ƙashin bayan duk wani ɓata da wata bidi'a a wannan duniya, tun daga kan Ibilis har ƙarshen duniya. Ba don shubuhohi ba da ba a samu wani kafirci ko bidi'a ko munafunci ko fasiƙanci ba a duniya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user