Tuesday 6 August 2024

Sirrin Yadda Ake Bayyana Soyayya Ga Saurayi Ko Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Ana isar da saƙon soyayya ta hanyoyi da dama, wasu hanyoyin sun haɗa da wasiƙa da zuwa da kai, su ne hanyoyi mafi dacewa ko mafi ƙarfi da aka fi isar da saƙon soyayya kuma aka fi saurin gasgata cewa lallai wanda ya isar da wannan saƙo na soyayya  ya kamu matuƙa.


Bayyana soyayyar ku
Hoto: Independent


MarubuciImran Musa Jahun


NA MAZA


Zuwa da kai ya fi saƙo, shi ne mutum ya shirya, musamman ya je gidan su wadda ya gani yake so ya tura a kirawo ta, cikin shigar kamala, da nuna halin kawaici.


Idan ta fito ka isar mata da saƙon da kake tafe da shi, cikin kyakkyawan lafazi da tausasa murya, kada ka sanya ƙarya a zancenka ko batun da hankali ba zai ɗauka ba, ƙwaƙwalwa ba za ta amince da shi ba.


Abin da ya kamata ka fara shi ne ka gabatar da kanka a gare ta.


MISALI


Sunana Imran,  ba don komai na zo gare ki ba face sai don na isar miki da saƙon da nake ɗauke da shi a cikin zuciyata.


Wanda wata ƙila ya yi miki daɗi ko akasin hakan.


Na san kin san cewa Allah ta'ala shi ne wanda ya halacci soyayya, sannan ya sanya ta a tsakanin halittunsa, musamman ga jinsin mace da namiji walau Namiji ya kamu da son Mace ko Mace ta kamu da son Namiji.


To ni dai ina daga cikin waɗanda Allah ya yi

halittar so a zuciyarsu.


A wannan lokaci, a sanadin ganin ki, jin sautinki, tarbiyarki, halayenki, musamman tarbiyarki da kuma iliminki.


Saboda waɗannan halaye naki na zo domin na isar miki da saƙon zuciyata zuwa gare ki, zuciyata ta kamu da soyayyar ki, a sakamakon gamsuwa da ta yi da tarbiyarki, kuma ta ga dacewar ƙulla alaƙar  soyayya da ke.


A taƙaice wannan shi ne saƙon da nake ɗauke da shi.


Zan so ki aminta da ni, ki ba ni damar zuwa

gare ki, wata ƙila zuciyar ki ta aminta da ni kamar yadda tawa ta aminta da ke.


Wannan ita ce kawai alfarmar da nake nema a gare ki.


NA MATA


Mace ma tana iya isar da saƙon soyayyar ta kwatankwacin hakan, ta hanyar zuwa wajen wanda ta kamu da soyayyar sa ta isar masa da saƙonta, wata ƙila kunya ta hana ta, don haka sai ta rubuta wasika.



MISALI


Assalamu alaikum, bayan shimfiɗaɗɗiyar sallama wadda addinina ya tanadar, ya harkokin yau da kullum ya lafiyarka?


Bayan haka, kada ka yi mamakin ganin wannan wasiƙa tawa, ko kuma Shaiɗan ya yaudare ka cewa kada ka amince da ni domin na yi tallan kaina a gare ka.


Sam-sam kada ka yarda da hakan, ya zo a

hadisin Manzon Allah ( S. A. W) cewa a zamaninsa mata suna zuwa ga maza suna neman amincewar su domin su yi aure, don haka neman soyayyar namiji a wajen mace ba rashin aji ba ne, ko zubar da kima.


Wannan shi ne cikakken aji da kyautatawa, domin mun yi koyi ga bayin Allah na gari.


Sunana Khadijah, wataƙila ka san ni, wata

ƙila kuma ba ka san ni ba.


A wata rana ina tafiya na haɗu da kai a hanya, cikin ikon Allah sai na ji na kamu da soyayyarka sakamakon ganin tsananin kamalarka, ilimi, hankalinka, ga tsafta.


Zuciyata ta aminta da kai, ta fara azabtar da

gangar jikina.


Lallai ina buƙatar agaji daga gare ka, don haka zan so ka ziyarce ni.


Zan ci gaba daga inda na tsaya a mako mai zuwa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user