Wednesday 7 August 2024

Tarihin Shaidan Da Ma'anar Sunan Shi

Tura Wannan Zuwa Ga

Sheɗan suna ne ko siffa ce da ake kiran Iblis da shi, wanda asalin sa daga wuta aka halicce shi, daga jinsin aljanu, an kira shi da suna iblis a gurare goma sha ɗaya a cikin Alkur'ani mai girma, kuma  halitta na farko daga cikin aljanu wanda ya fara bijrewa umarnin Allah ta'ala, na ƙin yin sujjada ga Annabi Adam (AS.).


Asalin Shaiɗan
Hoto: Mythos and legends fandom


MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


Kuma ana amfani da wannan suna ko siffa a kan dukkan aljani ko mutum, wanda ya kangare ya yi tawaye ko ya zama cikin miyagu, har dabbobi idan suka ɗauki wata siffa mara kyau a na kiransu Sheɗanu, kamar yadda Annabi (S.A.W) ya kira baƙin kare da sheɗan.


Sheɗani shi ne babban abokin gabar musulmi mumini, ba shi da wani aiki dare da rana sai ƙoƙarin halakar da shi da taɓar da shi, da nuna mummunan abu a cikin sura mai kyau da nuna kyakkyawan abu a cikin sura mummuna, da sa masa kasala wajen yin aiki mai kyau, da kuma sa masa nisaɗi a wajen aikata mummuna, domin ya  raba shi da imaninsa ko ya rage masa shi ta hanyar saɓo, da duk hanyar da ya samu dama ko ƙarama ko babba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user