Sunday 15 September 2024

Kada Ka Tada Hankalin Ka Saboda Su

Tura Wannan Zuwa Ga

A cikin rayuwa akwai wani lokaci da wasu mutane za su raina ka, ba za su gan ka da darajar komai ba saboda ba ka da abin duniya. 


Kada Ka Tada Hankalin Ka Saboda Su
Hoto: The Conversation

Marubuci:- Abdul-hadee Isah Ibraheem


Ba ka da abin da za ka bayar ma kowa, amma nan gaba a cikin rayuwa idan Ubangiji ya amince za a kai lokacin da za su so a ce sun mallaki hoton ka don su nunawa duniya cewa sun taɓa sanin ka ko sun taɓa yin wata alaƙa da kai a cikin rayuwa.


Kar ka tayar da hankalin ka don mutane sun ƙi girmama ka, saboda ba ka da komai a yau, za ka ga hatta iyayen ka abun ya kan shafe su, babu wanda zai yi wani abu don ya girmama mahaifin ka ko mahaifiyar ka.


Amma idan ka yi haƙuri, ka daure ka dage akan abin da ka sa a gaba, za a zo lokacin da mutanen da suke raina matsayin ka za su so a ce sun riƙe ka hannu bibbiyu a lokacin da kake faɗi tashi a cikin rayuwa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user