Friday 13 September 2024

Gajerun Kalaman Barka Da Juma'a Zuwa Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Kowacce rana tana zuwa da salon nata farin cikin muddin soyayyar ki na shimfiɗe a zuciyata. Masoyiya annurin zuciyata, ina kula da duk wani motsi na zuciyar ki da take wajena.


Kalaman Barka Da Juma'a Zuwa Ga Masoyiya
Hoto: Freepik

Ki sani na adana zuciyar ki da kika ba ni, a ma'adana mafi sirrin sirrantuwa da ɓoyuwa daga dukkan halittu.


Haƙiƙa za ki alfahari da ni, kin damƙa amanar zuciyar ki ga wanda ba zai taɓa cutar da ita ba daidai da daƙika guda ko rabin daƙika.


Ina alfaharin samun masoyiya kamar ki mai cike da kyawun zuciya, kyan fuska da sura.


Salon iya magana da salon iya tafiya, haɗe da sabon salon soyayyar zamani mai cike da ƙarawa wutar soyayyar da ke ci a zuciya fetur.


Fara'a da murmushi ɗauke a fuskata ina kallon kyakkyawar fuskar ki nake cewa Barka Da Safiyar Juma'a masoyiyata.


Dan Love ne ya gabatar da su ta hanyar Audio, wakilin mu kuma ya fitar da su a rubuce don jin daɗin ku da nishaɗin ku.


Za ku iya latsa nan yanzu domin sauke zafafan kalaman soyayya na saurare kawai.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user