Friday 13 September 2024

Ire-iren Kyau Da Ma'anonin Shi

Tura Wannan Zuwa Ga

Kyau iri uku ne; kyawun hali, da kyawun zuciya sai kuma kyawun fuska.


Ire-iren Kyau
Hoto: Boss


Marubuci:- Tasi'u Rufa'u Musa Gumel


 1. Kyawun hali, wani nau'i na kyau ne wanda yake jagorantar ma'abocinsa zuwa tafarki mai kyau zai bambanta a cikin al'umma.


Kuma yana kusanta shi da al'umma har wasu suke ƙoƙarin koyi da shi, daga ƙarshe ya kan iya kai sa ga wata hanya madaidaiciya.


2. Kyawun zuciya shi ne mafi kyau  a cikin rukunin kyau domin yana jagorantar ma'abocinsa zuwa tafarki madaidaci, ya kusanta shi da Ubangiji, ya ɗaukaka darajarsa a cikin al'umma har ya samu dacewa daga duniya zuwa lahira. Ubangiji Allah ya datar da mu Amin. 


3. Kyawun fuska shi ne mafi hatsari a cikin jerin kyau domin yawanci ya kan halakar da masu shi.


Wasu kuma ya kan jefa su cikin wata matsala wacce za ta iya wargaza rayuwarsu baƙi ɗaya. Ubangiji Allah ya kiyaye mu Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user