Saturday 21 September 2024

Karanta Gajerun Kalaman Kiran Waya Na Soyayya

Tura Wannan Zuwa Ga

Ina jin cewa na gama samun wacce ta cancanta cikin 'yammata, kuma ina jin cewa na gama kai wa maƙurar ƙarshe, lalubena ya tsaya cak a kanki gimbiyar mata, a yanzu ba ni da wani sauran zaɓi a zuciyata. Ke ce kawai ke yin yadda kike so a cikin ta.


 Gajerun Kalaman Kiran Waya Na Soyayya
Hoto: Freepik

Marubuci:- It'z Nazeephancy DH

Haƙiƙa kin mallake komai daga gare ni mallaka ta dindindin, babu lokaci, sannan kuma babu yanayi, dukkanninsu ke ce kike bayyana a gare ni cikin zallar ƙauna da soyayya. 


Zan yi yaƙi, kuma zan dage tare da jajircewa a kan soyayyarki, saboda ke ce kawai ke gare ni cikin 'yammata, kuma ke ce kaɗai ke iya gamsar da zuciyata farin ciki mai tattare da nishaɗin soyayya.


Ke ce zaɓina ta farko sannan ke ce ta ƙarshe, ƙuri'ata dukka tana gare ki masoyiyata.


Gare ki na sallama komai nawa, kuma ina da tabbacin na zo inda ya dace.


Fatana ki kasance tare da ni, ina tabbatar miki da samun farin ciki mai ɗorewa. Ina son ki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user