Saturday 21 September 2024

Sirrikan Yadda Za Ka Gina Rayuwar Ka

Tura Wannan Zuwa Ga

A dai dai lokacin da kake so ka gina kanka, kar ka damu da abubuwa huɗu:


1. Kar ka damu da sai lallai mutane sun fahimce ka, kar ka damu mutane su girmama ka a yau, ka ƙyale su da fahimtar su a kanka a yau.


Yadda Za Ka Gina Rayuwar Ka
Hoto: Iol

Marubuci:- Abdul-hadee Isah Ibraheem


2. Kada ka damu da kwalliya, ado, sayen kayan burgewa da nuna kai wani ne. Wannan ba naka ba ne a dai dai lokacin da kake son gina kanka irin ginin da nan gaba za ka gina wasu.


3. Kar ka damu da lallai sai ka yi wadataccen baccin da ranka yake so. Matuƙar ka bayar da muhimmanci wa bacci a shekarun da kake son gina kanka to kana tone ramin da za ka faɗa ciki ne.


Kada ka bi  masu son jiki da son hutawa a lokutan dare da rana. Ka yi baccin da jikin ka yake buƙata kawai.


4. Ka yi haƙuri da cewa sai fatar ka ta yi kyau, ko sai surar jikin ka ta yi kala kaza ko kamanni kaza. A cikin shekarun da kake gina kanka dole rama za ta kama ka, za ka rame za ka canza, idon ka zai yi ja a wasu lokuta saboda gajiya da rashin bacci da fafutuka.


Wasu za su ɗauka ba ka da lafiya ne, amma kai ka san lafiyar ka lau, fafutuka ce kawai, saboda kana da wata manufa, kana da wani wajen da kake so ka isa kafin ka huta.


Dole sai ka sadaukar da wasu shekaru a cikin rayuwa, ka wahala a cikin su, daga baya wasu shekaru za su zo waɗanda za ka dinga tuna wancar wahalar da ka sha a baya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user