Sunday 8 September 2024

Karanta Gajerun Sakonnin Barka Da Karshen Mako

Tura Wannan Zuwa Ga

Ke ce abincin ido da zuciyata, ina sonki ina da burin kasancewa tare da ke har ya zuwa lokacin ƙarshen rayuwata. Ina sonki.


Gajerun Sakonnin Barka Da Karshen Mako
Hoto: Move me quotes


Marubuci:- It'z Nazeephancy DH


A cikin rai da zuciyata kin cancanci na fara yi miki sallama cikin sanyin murya mai ɗauke da kalaman soyayya zalla zuwa ga autar mata kamar ki.


Bayan saƙon gaisuwa ya samu isa zuwa wajen da nake buƙata, sai na nemi alfarma guda ɗaya daga gare ki.


Don Allah ina so ki yi mini masauki a kusa da ke domin na ji daɗin karanta miki karatun cikin zuciyata mai tafiya da taken tambarin ina fatan kina lafiya.


Uhmm murmushi nake a gare ki tare da kallon haƙoranki masu sheƙi kamar zinare, cikin yanayin haka ne na zube a gaban ki ina ladabin isar da saƙon ƙaunata zuwa gare ki.


Lallai na kamu da son ki ta hanyar da ban san farkon ta ba, a duk lokacin da zan yi numfashi ina shaƙar iskar da ke ɗauke da ƙaruwar son ki a raina.


Linƙayar yayyafin ruwan samaniyar sammai idan yana sauka a cikin duniya babu abin da nake ji sai saukar son ki wanda nake jin shi daidai da yadda ruwa yake saukowa.


A gaskiya kin haɗu kuma kin tsaru bisa tsarin tafarki mai kyau, ta haka ne kike tsara yanayin rayuwarki ba tare da kina zullumin komai ba.


Harsashin son ki ya taho da zafin ƙaunarki cikin lokacin da nake tunaninki sai kawai na ji ya soke ni a daidai wajen da babu mai iya cire shi.


Idaniyata ta daɗe da makancewa ba ta iya ganin komai wanda ba shi da alaƙa da ke tabbas ke ce ruhin da ke raya farin cikin zuciyata ina ƙaunarki Habibty.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user