Monday 9 September 2024

Karanta Ka'idodin Tuba Ga Musulmai

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Mutum ya yi nadama a kan abin da ya faru. Ma'ana ya yi nadama cewa abubuwan da suka faru da shi ba zai sake ba, wato bai ji daɗin abin da ya faru ba. Shi ne ma'anar:

الندم على ما فات


Ka'idodin Tuba Ga Musulmai
Hoto: About Islam

MarubuciAbbati Mai Shago Flg


2. Da kuma niyyar cewa ba zai koma zuwa ga wannan zunubin ba a cikin abin da ya ragu na rayuwarsa.


3. Sannan kuma ya bar aikin saɓon a daidai lokacin idan yana cikinsa.


Allah (S.W.T) a cikin Suratut Tahrim yana cewa:

يأيها الذين ءامنوا توبوا إلى الله توبة نصوحة


"Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku tuba zuwa ga Allah tuba ingantacce".


Don haka a nan gurin abin tambaya shi ne mene ne ma'anar tuba ingantacce?


Tuba ingantacce shi ne wanda ya cika waɗannan sharuɗɗa guda uku:


Mutum ya yi nadama, ya yi niyyar ba zai sake yin wannan zunubin ba, ya kuma bar zunubin a lokacin take.


Kar mutum ya dinga ci-gaba da zunubi kuma yana cewa yana tuba zuwa ga Allah (S.W.T). Idan mutum yana so ya yi cikakken tuba ya yi tuban da ba zai sake komawa zuwa ga zunubin ba. Shi ne ma'anar:


والنية أن لا يعود إلى ذنب فيما بقي عليه من عمره.


Mutanen ƙwarai a yadda suke yin rayuwarsu shi ne za ka ga mutum yana bautawa Allah (S.W.T) kamar inda za a ce gobe zai mutu ba zai yi ƙari sama da abin da yake yi ba.


Manazarta


Fassarar Littafin Ahlari Tare Da Sharhin Ma'anoninsa Zuwa Harshen Hausa Na Dr. Jamilu Yusuf Zarewa shafi mai lamba 47-48.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user