Monday 9 September 2024

Rubutacciyar Wakar Soyayya Ta Begen Masoyin Gaskiya Ta Shamsiyya Sadi

Tura Wannan Zuwa Ga

A! Babu abin da ke damuna.


In dai da kai masoyin raina.


Na sha wuya cikin soyayya kafin ka zo garan angona.


So ya bi jiki da tunani kai na saka cikin ƙalbina.


Na samu jarumi mai tsafta, shi ne kaɗai cikar burina.


Waƙar Soyayya Ta Begen Masoyin Gaskiya
Hoto: Self

Idan har na kwanta, kai ne kake zuwa cikin barcina.


Da murmushi ka doso guna.


Kana faɗin me ke damuna?


Cikin shagwaɓa zan amsa ba ka kaucewa ganina.


Idan har na farka ji nake ba ya ni a wannan rana.


Ƙamshin ka ya ɗeben kewa, koda ga ido kwai nisa.


Takun ka abin burgewa a kanka za na ɗau duk fansa.


Maganar ka babu hayaniya, kalaman ka sai ka tausa.


Ya zan ji idan na rasa ka, auren mu ni da kai na ƙosa.


Na ba ka amanar kaina, musu da kai ba za na iya ba.


Da ka yi kirana zan zo, nisa da kai ba za na iya ba.


Matso guna ya masoyi, ni zan yi ma wata simba.


Burina na sa ka a shauƙi, ba ka tuna da wata ɗiya ba.


Da zan san kalmar ƙauna da ba ya ita wannan duniya.


Da zan furta maka duk dai da kai ɗin ina jin kunya.


Ni na san ina ƙaunar ka, kuma zan yi ma biyayya.


Za na tarairaye ka ya jariri zo na ɗora ka a baya.


Ƙawaye suna tambayata wanne irin so ni nake ma?


Na so kwatanta shi na kasa ni dai na sani yai girma.


Ba na iya komai yanzu, tamkar kifi kan koma.


Allurar nan ka sa min ba mai musun hakan in gaya ma.


Saƙon zuci na furta ma ko ba amsa na ji daɗi.


Burina kawai ka ji shi hakan kaɗai ya sa ni nishaɗi.


Ka maida ni sarauniya yanzu, a wagga duniya mai faɗi.


Abin burgewa guna da ni da kai muna yin taɗi.


Kalmar so ba ta burge ni in ba daga kai ta fito ba.


Sunana bai min daɗi in ba kai ka furta ba.


Farin ciki koda na yi in ba kai ka sa ni na yo ba.


Sai na ji damuwa ta rufe ni kallon ka ba zan ƙosa ba.


Kallon ka ba zan ƙosa ba.


Na gode Allah Rabba shi ne ya ba ni kai mai sona.


Ba wayo babu dabara cikin samun ka gurina.


Zan yi sallah na roƙi Buwayi ya ba ni kai ka zamma mijina.


Nai salati gun Manzo shugabana.


Gatana!!


Shamsiyya Sadi ce ta rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi ku. Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user