Saturday 28 September 2024

Karanta Tarihin Rayuwar Hassan Nasrallah

Tura Wannan Zuwa Ga

An haifi Sheikh Hasan Nasrallah ne dai a ƙauyen Karanteena na ƙasar Labanon, a Ranar 31 Ga Watan Augusta 1960, mahaifinsa kuwa ɗan kasuwa ne mai sayar da 'ya'yan itace don amfanin al'ummar yankin tare da yayan Nasrallah ɗin, a wasu lokuta kuma Shiekh Hasan shi ma ya kan je wajensa don taimaka masa. A irin wannan zuwa da yake yi ne wata rana ya ga hoton Imam Musa al-Sadr, sanannen malamin nan na ƙasar Labanon ɗin da ya ɓace a ƙasar Libya kuma har ya zuwa yanzu ba a san inda yake ba, wannan hoto dai ya yi tasirin gaske a zuciyar Nasrallah inda har ya yi fatan shi ma da a ce wata rana zai zamanto kamar wannan malami da kuma fatan ya kasance daga cikin mabiyansa saboda irin haiba da alamun taƙawa da ke tattare da shi.


Tarihin Rayuwar Hassan Nasrallah
Hoto: Aljazeera

MarubuciSaliadeen Sicey


Hassan Nasrallah dai tun yana ƙarami bai kasance kamar sauran yaran ƙauyen nasu da suke zuwa wasan ƙwallo, iyo da dai sauransu ba, saɓanin haka ya kasance ya kan lizimci zuwa masallaci duk da cewa shi dai ba shi da alaƙa da wani malami na musamman, amma dai duk da haka ya kasance mai kula da al'amuran addini. Irin wannan yanayi nasa ne ma ya sanya ya kan zauna shi kaɗai tare da hoton Imam Musa al-Sadr saboda mafi yawan al'ummar garin ba su damu da lamuran addini ba.


Lokacin da ya ɗan data, wato kimanin shekaru tara a duniya, Shiekh Hasan ya kan je wata 'yar kasuwa da ake sayar da gwanjon littattafai don ya saya da kuma karantawa, musamman ma dai littattafan da suka shafi addini, duk da cewa dai ba ya fahimtar dukkan abin da ya karanta saboda ƙarancin shekaru, to amma dai ya kan ajiye waɗannan littattafan da nufin cewa nan gaba zai sake karanta su da kuma fahimtar abin da suka ƙunsa. A daidai wannan lokaci da Nasrallah ya ke ci gaba da wannan bincike yana makarantar elementare ne a makarantar al-Najah da ke yankin nasu. A shekarar 1970 ne dai ya gama wannan makaranta da kuma shiga makaranta ta gaba a Sinelfeel da ke garin Sur. Bai dai samu ya gama wannan makaranta ba saboda ɓarkewar yaƙi a ƙasar Labanon ɗin a shekarar 1975, lamarin da ya tilasta wa iyalansa barin wannan gari da komawa ƙauye.


Hassan Nasrallah ya fara shiga wata ƙungiya ce dai a lokacin da ya koma garin Bazouriya inda ya shiga cikin ƙungiyar Amal ta Imam Musa al-Sadr saboda irin alaƙa da kuma ƙaunar da ya ke wa Imam Musa ɗin a lokacin kuwa yana ɗan shekara 15 ne a duniya, ita dai wannan ƙungiyar ta Amal ana mata laƙabi da "Ƙungiyar Marasa Galihu", duk da cewa a wannan gari nasu dai ƙungiyoyin kwaminisanci da Markisanci ne suka fi samun gindin zama. Bayan zamansa ɗan ƙungiyar Amal tare da wansa Husain Nasrallah, an ba shi matsayin wakilin ƙungiyar na wannan gari duk kuwa da ƙarancin shekarun da ya ke da shi.


Bayan ɗan wani lokaci dai, Hasan Nasrallah ya ƙudiri aniyar tafiya birnin Najaf al-Ashraf na ƙasar Iraki don karatun addinin Musulunci a lokacin kuwa yana ƙasa da shekaru 16 ne a duniya. Bayan da ya yi wannan ƙuduri sai ya tafi garin Sur inda ya sadu da wani malami da ke wakiltar Imam Musa al-Sadr a garin mai suna Sayyid Muhammad al-Garawi don tattaunawa da shi kan yadda zai cimma wannan buri nasa na tafiya garin Najaf ɗin. Jin haka sai Sayyid al-Garawi, wanda daman yana da alaƙa da kuma sanayya da Shahid Sayyid Muhammad Bakir al-Sadr, babban malamin garin Najaf ɗin na lokacin, sai ya rubuta wa Shahid al-Sadr ɗin wasiƙa da bayyana masa irin ƙwazon Nasrallah don ya ba shi daman karatu a Najaf ɗin.


Bayan 'yan shirye-shirye, sai Hassan Nasrallah ya yi bankwana da iyalansa ya kama hanyar Najaf, koda ya isa sai ya tafi inda 'yan ƙasar Labanon su ke da nufin su taimaka masa isar da wasiƙar da take tare da shi ga Shahid al-Sadr, inda Sayyid Abbas Musawi, wanda daga baya ya zamanto shugaban Hizbulllah, ya karɓi wasiƙar da nufin isar da ita zuwa ga mai ita, wannan dai ita ce farkon alaƙar Nasrallah da Sayyid Abbas al-Musawi. Bayan isar da wannan wasiƙa dai, Shahid al-Sadr ya yi maraba da Hassan Nasrallah, inda ya buƙaci Sayyid Abbas al-Musawi da ya sama masa wajen zama da kuma ci gaba da koyar da shi, ta haka ne Sayyid Abbas al-Musawi ya zamanto malami kana kuma mai shiryar da Sayyid Nasrallah, wannan alaƙa da ta ci gaba da wanzuwa har lokacin da Sayyid Abbas din ya yi shahada lokacin da sojojin yahudawan sah-yoniya suka kai masa hari da tarwatsa motar da yake ciki.


Da yake Sayyid Abbas ya yi nisa a karatunsa a lokacin, don haka sai Shahid al-Sadr ya ware masa aji don koyar da ƙananan ɗalibai, inda daga cikin ɗaliban har da shi Nasrallah. Saboda irin ƙwazon da Sayyid Abbas ya ke da shi ya sanya ɗaliban nasa sun yi karatu mai yawan gaske cikin ɗan karamin lokaci.


A shekarar 1978 Nasrallah ya gama kashin farko na karatun nasa yana mai shauƙin ci gaba da karatunsa a wajen wannan malami nasa da ya kasance masa tamkar uba, to sai dai kuma wani gagarumin al'amari ya faru da ya kusan kawo ƙarshen wannan karatu nasa. Wannan lamari kuwa shi ne faruwar wani gagarumin shiri da gwamnatin Iraki ta wancan lokaci ta fara na korar ɗaliban Hawza 'yan ƙasashen waje da suke karatu a Irakin suna masu zargin wasu da kasancewa jami'an leƙen asirin ƙasar Siriya wasu kuma suna da alaƙa da wasu ƙungiyoyin Musulunci.


Wannan lamari ne dai ya sa jami'an tsaron Irakin suka kai hari ga makarantar Hawza ta birnin Najaf da kame wasu ɗalibai, inda bayan tsare su na wani lokaci suka kore su da dama kuwa daga cikinsu 'yan ƙasar Labanon ne. A daidai lokacin da jami'an gwamnatin Saddam ɗin suka zo kame ɗaliban kuwa, Sayyid Abbas Musawi ba ya cikin ƙasar Iraki ya tafi hutu Labanon don haka aka shawarce shi da kada ya dawo don ana nemansa ruwa a jallo. A nasa ɓangaren shi ma Nasrallah ba ya makarantar lokacin da aka zo wannan kame, don haka bayan da ya dawo aka gaya masa labarin kame 'yan'uwansa, sai aka shawarce shi da shi ma ya gudu, inda kafin jami'an tsaron su ankara ya samu damar ficewa daga Irakin da kuma komawa gida.


Bayan komawarsa gida ma, Nasrallah ya ci gaba da karatunsa a wajen Sayyid Abbas Musawi a makarantar da ya buɗe, a daidai lokacin da kuma ya ke karantarwa a ita dai wannan makaranta. Baya ga karatu da kuma karantarwar, Sayyid Nasrallah ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a wannan kungiya ta Amal, inda ma aka zaɓe shi a matsayin wakilin ƙungiyar na ɓangaren siyasa a garin Bikaa.


A shekarar 1982, bayan mamayan da ƙasar Isra'ila ta yi wa ƙasar Labanon, an samu kafuwar wasu ƙungiyoyi masu son fada da wannan mamaya, to sai dai kuma saboda wasu dalilai da suka yi ta bijirowa ya sanya an samu rabuwar kai tsakanin 'yan wannan ƙungiya ta Amal, inda wasu daga cikinsu suka fice suka kafa ƙungiyar Hizbullah daga cikin waɗanda suka ɓalle ɗin kuwa har da Sayyid Nasrullah. Babban take da burin ƙungiyar Hizbullah ɗin dai shi ne kawo ƙarshen wannan mamaya ta yahudawa.


Duk da cewa dai daga farko-farkon lamurra Hasan Nasrallah bai kasance daga cikin majalisar gudanarwa ta wannan ƙungiya ta Hizbullah ba, to sai dai kuma ya riƙe muƙamai daban-daban a ƙungiyar da suka haɗa da shugaban reshen Ba'alabak daga baya kuma ya zamanto shugaban reshen Bika'a na ƙungiyar gwagwarmayar. Sannan kuma ya kasance mataimakin shugaban ƙungiyar reshen birnin Beirut, daga baya ma dai ya zamanto shugaban reshen Beirut ɗin bayan da shugaban reshen Sayyid Ibrahim Ameen Sayyid ya koma ɓangaren siyasa na ƙungiyar, hakan ya sanya ya kasance daga cikin manyan jami'an ƙungiyar na gaba-gaba. Duk da cewa dai Sayyid Hassan na son ci gaba da karatunsa, to sai dai kuma saboda wannan mamaya na yahudawa ya hana shi hakan saboda ayyukan fada da wannan mamaya. To amma a shekarar 1989, bayan samun izini daga ƙungiyar, Nasrallah ya nufi birnin Kum na ƙasar Iran don ci gaba da karatun nasa. A garin Kum dai Nasrallah ya yi karatu a wajen malamai daban-daban inda duk suke yaba masa saboda irin ƙwazon da ya ke da shi.


To sai dai kuma wannan karatu nasa a Kum bai jima ba saboda kisan gillar da yahudawan sahyoniya suka yi wa Sayyid Abbas al-Musawi, shugaban ƙungiyar ta Hizbullah a shekarar 1992, wannan ɗanyen aiki dai ya tilasta masa dawowa gida. Bayan jana'iza da zaman makoki dai majalisar gudanarwa ta ƙungiyar Hizbullah ɗin ta zaɓi Sayyid Hassan Nasrullah a matsayin shugabanta, saboda irin ƙwazonsa da kuma kusancin da yake da shi da Shahid Abbas al-Musawi, kuma wannan muƙami ne ya ke ci gaba da riƙewa har zuwa lokacin kashe shi.


Hassan Nasrullah dai ya yi aure ne a shekarar 1978, inda ya auri Fatima Yasin wacce ta fito daga garin al-Abbasiya da ke yankin Sur. Ya zuwa yanzu dai Sayyid Nasrallah yana da 'ya'ya huɗu, wato Hadi, wanda ya yi shahada a yayin bata kashi da sojojin  ƙasar Isra'ila a lokacin yana ɗan shekaru 18 a duniya, sai kuma mai biye masa wato Muhammad al-Jawad, sai kuma Zainab sai kuma na ƙarshensu Muhammad Ali.


Kisan Ɗan Nasa Muhammad hadi


A daren 12/13 ga watan Satumban shekarar 1997 aka kashe mayaƙan Hizbullah huɗu a wani harin kwantan ɓauna da Isra'ila ta kai kusa da Mlik. Ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu shi ne Muhammad Hadi mai shekaru 18, babban ɗan Nasrallah. Sojojin Lebanon biyar da wata mace sun mutu a wani harin da aka kai ta sama a lokaci guda a arewa da 'yankin tsaro'. Ana kallon hare-haren a matsayin martani ga farmakin da aka kai mako guda da ya gabata inda aka kashe kwamandojin Isra'ila goma sha biyu. An ruwaito Nasrallah yana cewa yayin da yake samun labarin rasuwar ɗansa "Ina alfahari da kasancewa mahaifin ɗaya daga cikin shahidai."


Daya Cikin Maganganunsa


"Idan har za mu kori mamayar Isra'ila daga ƙasarmu, ta yaya za mu yi haka? Mun lura da abin da ya faru a Falasɗinu, a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan, da Zirin Gaza, da Tuddan Golan, da Sinai, mun cimma matsaya kan cewa, ba za a iya dogaro da ƙasashen Larabawa ba, ko kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ....Hanya ɗaya tilo da muke da ita ita ce mu ɗauki makamai mu yaƙi dakarun mamaya."


A wata hira da jaridar Washington Post, a shekara ta 2000, Nasrallah ya ce "Ni ina adawa da duk wani sulhu da Isra'ila. Ban ma yarda da kasancewar wata ƙasa da ake kira 'Isra'ila ba." Ina ganin kasancewarsa a matsayin rashin adalci da kuma haramun, shi ya sa idan Lebanon ta ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila, kuma ta kawo wa majalisar dokoki hakan, wakilanmu za su yi watsi da ita, Hizbullah ta ƙi amincewa da duk wani sulhu da Isra'ila bisa manufa."


A shekara ta 2006, Nasrallah ya ce "Babu mafita ga rikici a wannan yanki face ɓacewar Isra'ila."


Da yake magana a ranar Kudus a ranar 2 ga Agusta, 2013, Nasrallah ya ce Isra'ila "ƙasar daji ce da dole ne a kawar da ita."


An yi zargin yunƙurin kashe Shi a shekarar 2008


Almalaf, majiyar labaran Iraki a ranar 15 ga watan Oktoban 2008, ta naƙalto majiyoyi daga ƙasar Lebanon na cewa an sakawa shugaban ƙungiyar Hizbullah Hasan Nasrallah guba a makon da ya gabata, kuma likitocin Iran da suka je Labanon domin yi masa magani sun cece shi. Majiyar ta shaida wa jaridar cewa an yi amfani da wani sinadari mai guba musamman kan shugaban mayaƙan na Shi'a. Da alamu dai yanayin lafiyarsa ya yi tsanani na tsawon kwanaki har sai da likitocin Iran suka zo suka yi nasarar ceto rayuwarsa. Almalaf ya yi iƙirarin cewa majiyoyin sun yi imanin cewa akwai yiwuwar sanya gubar wani yunƙuri na kashi da Isra'ila ta shirya ne.


Hezbollah ta musanta cewa an saka wa Nasrallah guba. Ɗan majalisar dokokin ƙasar Labanon Al-Hajj Hassan ɗan ƙungiyar Hizbullah ya ce: "Wannan ƙarya ce da ƙage-ƙage, gaskiya ne ban ga Nasrallah a cikin makon da ya gabata ba, amma ba shi da lafiya." Likitocin na Iran sun isa ne a ranar Lahadin da ta gabata da misalin ƙarfe 11:00 na dare, bisa dukkan alamu cikin wani jirgin soji na musamman. A cewar jami'an Almalaf sun yi la'akari da tashin Nasrallah zuwa Iran don ci gaba da jinya.


Mutuwa


A ranar 27 ga Satumba, 2024, sojojin saman Isra'ila sun kai wani hari ta sama kan hedkwatar Hezbollah da ke Beirut, wanda aka ce sun nufi Nasrallah. Aƙalla mutane shida ne suka mutu sannan sama da 90 suka jikkata sakamakon harin, yayin da wasu da dama suka ɓace.


A safiyar ranar 28 ga Satumba, 2024, IDF ta bayyana cewa Nasrallah ya mutu a harin. Sa'o'i kaɗan bayan haka, Hezbollah da hukumomin Lebanon sun tabbatar da mutuwar Nasrallah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user