Friday 20 September 2024

Kyawawan Sakonnin Barka Da Juma'a Ga Masoyi

Tura Wannan Zuwa Ga

Masoyi, yau farar rana ce da ke faranta fararen zukata, musamman irin mu fararen masoya masu farin ƙudirin da ke haskaka duniyar masoya ta yi fari.


Kyawawan Sakonnin Barka Da Juma'a Zuwa Ga Masoyi
Hoto: Zerographic

Cikin shauƙin so ɗauke da murmushi mai sanyi ina kallon fuskar ka nake cewa Barka Da Juma'a masoyina mai faranta zuciyata, fatan ka yi sallah lafiya? Tare da addu'ar Allah ya ƙara rura wutar ƙaunar junanmu a zukatan mu bakiɗaya.


Masoyina da a ce ana bada aron ido da na ba ka aron idona domin ka kalli kanka ka ga irin kyawun da ka ƙara fiye da na kowacce rana. Na san cewa idanuna ne kaɗai ke ɗauke da sirrin ganin wannan ɓoyayyen kyawun naka wanda da man su kaɗai ya dace su kalla.


Masoyina ba tare da gajiyawa ba zan iya kwana na kuma wuni ina kallan kyawun nan naka mai ƙayatarwa, musamman idan ka saki murmushi haɗe da limshe fararen idanuwan nan naka masu fisgar zuciya da ruhina a duk lokacin da na kalle su.


Dan Love ne ya gabatar da su ta hanyar Audio, wakilin mu kuma ya fitar da su a rubuce don jin daɗin ku da nishaɗin ku.


Za ku iya latsa nan yanzu domin sauke zafafan kalaman soyayya na saurare kawai.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user