Monday 28 October 2024

Karanta Addu'a Idan Mai Azumi Zai Buɗa Baki

Tura Wannan Zuwa Ga

ذَهَبَ الظَّمَأُ، وَابْتَلَّتِ العُرُوقِ، وَثَبَتَ اْلأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللهُ.


Zahabaz-zama-o wabtallatil-'urooq, wathabatal- ajru in shaal-lah.


Ƙishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah Ya so.


Addu'a Idan Mai Azumi Zai Buɗa Baki
Hoto: Mother


Abdullahi bn Amr bn Al-As ya ce Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Mai azumi yana da addu'a da ba a mayar da ita idan ya zo buɗe baki". 


Abdullahi bn Amr ya kasance idan ya zo buɗa baki sai ya ce;


اللّهُمَّ  إِنَّي أَسْأَلُكَ بِرَحْمَتِكَ الّتي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ، أَنْ تَغْفِرَ لِي .


Allahumma inne as-aluka birahmatikal-latee wasi'at kulla shay'i, an taghfira lee.


Ya Allah! Ina rokon Ka saboda Rahamarka da ta yalwaci komai, Ka gafarta mini.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user