Sunday, 17 November 2024

Ire-iren Ustazai Tare Da Zahirin Halayen Su

Tura Wannan Zuwa Ga

Wane ne Ustazi?


Ustazi shi ne duk wani mutum mai ƙoƙarin kiyaye dokokin Ubangijinsa gwargwado, da ƙoƙarin bin Umarnin Manzo (S.A.W) da kuma ƙoƙarin ganin ya siffantu da ɗabi'u na Manzo (S.A.W) daidai gwargwado.


Ire-iren Ustazai Tare Da Zahirin Halayen Su
Hoto: Deposit photos

MarubuciyaFatima Zahra


Kun san duk abin da aka ce hasashe da kuma abubuwan da ake gani a zahiri ne, ba zai yiwu ka zayyano su duka ba, sai dai ka kintata, akan samu mutum Ustazi ya haɗa dukkan abu ukun nan ko ya haɗa biyu ko ya haɗa ɗaya da rabin cikin ukun ko ya raba ƙafa da sauransu, mutum tara yake bai cika goma ba.


1. Bawan Allah! Yana ɗaki kusan kullum yana karatu, idan ka gan shi a waje ko wurin nema zai je ko wata ziyara ko masallaci ko majalisin wa'azi ko karatu ko makaranta ba ya magana sosai.


Da wuya ka ga yana da ko budurwa iyayensa yana musu biyayya iya yinsa, ƙannansa suna masa kallon tausayi haka yayyunsa, fatansu Allah kar ya haɗa shi da mace 'yar jaraba.


Idan yana da aure yawanci idan matar ba ta da kirki wahala yake sha, bai iya faɗa ba, bai iya cin zarafi ba, ko hayaniya ba ya so, kullum za ka gan sa a natse.


Yana ibada sosai, yana ƙoƙarin kiyaye haƙƙokin Allah a kansa, ya san soyayya amma ba ya iya ɗabbaƙa ta amma yana son a masa, yawanci mace ba ta iya masa soyayya sosai saboda shi yana da ɗabi'ar rashin karsashi, da sauran raha, za su zauna dai cikin za ta gaishe sa, za ta masa abinci da sauran haƙƙoƙi nashi amma da wuya ta iya masa oyoyo cikin annashuwa da zumuɗi, da wuya ta rinƙa masa shagwaɓa wani iri za ta dinga ji, sai ta ji kamar ba ya so, a'a yana so amma shi hakan yake.


Da yawansu kafin su ce suna son mace suna shan wuya, sun fi turawa sannan kuma sukan faɗa so ba tare da wacce suke so ta sani ba, saboda shi haka yake, sai an kai maƙura, kuma ba kowacce mace suke iya so ba, sai sun yaba da hankalinta matuƙa.


Irin ustazan nan ba su da matsala, sai dai ga mace sukan iya zama matsala, musamman idan ƙaramar yarinya ce, amma idan babba ce ba damuwa sosai.


Za ka gan shi da siffa ta kamala cikakkiya, ba ruwansa da cin naman mutane (gulma), shi bai san komai ba sai karatu, bai san komai ba sai ibada, yawanci za ka gan sa sallama yake wa mutane sai ya wuce abin sa, idan an ga yana magana ma ko wata hira har mamaki ake.


2. Bawan Allah mai abin mamaki, mai kwaikwayon kishi iri na Sayyadi Umar (R.A) akan iyali, ba sai an zurfafa ba amma kai daga ji ka san ruwa ba sa'an kwando ba ne, matarsa ta fi ƙarfin idon kwaɗayayye, har a wasu lokutan ta ji a duniya ba wanda ya kai shi takura mata saboda kishin ta da yake yi, nan da can idan za ta je idonsa akai tare da shimfiɗa mata sharuɗɗa da matakai, ta wani fannin kuma ta ga ashe yana tsananin son ta ne. Wannan abu biyu shi zai dinga yawo a zuciyarta, amma idan aka yi dace ita ma irinsa ce sai ta ji tsananin so ne da kula da iyali ya sa yake hakan sai ta ji hakan ya mata kuma ya burgeta.


Shi matarsa ba ta fita aiki, balle yawon kasuwanci, sai dai idan a cikin gida za ta yi, to wani ma na cikin gidan ba zai yarda ba, saboda ba ya son ta dinga cuɗanya da al'umma mabambanta.


Za ka gan shi da kwarjini, bai cika fara'a ba sosai sai ga wanda ya isa kuma ya dace, siffa ta kamala, da kuma sallama ga al'umma, mai saurin bayyana ustazancinsa ne a fili, yanzu-yanzu za ka ji yana maka Allah ya ce Annabi (S.A.W) ya ce koda yarensa yake magana sai ka ji kamar Larabci yake yi. A'a kawai saboda cuɗanya da kalmomin Larabci ne ya sa sai ka ji.


Misali: Idan Hausa ce sai ka ji yana sanya tafkim, tarƙiƙi, ƙalƙala, sugura da kubra, wani sai ya ɗauka yana sane yake yi.


Yana da ibada da son karatu sai dai mutane suna masa kallon ya cika tsauri da tsanani ko ƙannansa suna tsoron yin rashin ji a gabansa, da 'ya'yansa da matansa don an san ba zai ƙyale ba, haka kusan kowa yake ji idan ya gan sa, indai za a ɗan yi wata ƙiriniya sai a ɗaga ƙafa sai baya nan.


Yana da kirki ga wanda ya fahimcesa, zumunci da sauran abubuwa kyawawa sai dai wasu ba za su gane ba, saboda shagalallu sun fi yawa a cikin al'umma, irin wannan kuma matsalar irin wannan Ustazu yake samu a ɓangaren 'yan mata, saboda an san mata da son shagala sai dai idan an dace da samun irinsa.


'Yammata ba su cika son sa ba, saboda shi ba ya irin shirmen nan da 'ya mace ke so, kamar wankan matasan zamani da sauran shiririta, amma da ya yi arangama da irinsa sai ta ji ba wanda take so sai shi.


Iyayensa suna son sa saboda ba ya ɗauko musu magana, 'ya'yansa suna son sa saboda yana jan su a jiki da koyar da su ilimi da ibada, matarsa idan ba mai son duniya ba ce ita ma tana son abin ta ba ta jin irin abin da wasu matan irinsa suke ji saboda tsananinsa, yayyunsa da ƙannansa kuma ba a komai za su saka shi ba, saboda ya ƙware wajen hani da nummuna da umarni da kyakkyawa suna masa kallon kamar wani cikas, sai dai idan an yi sa'a yana da tarin dukiya. Ehim! To fa dole ma su saka shi a lamuransu.


3  Akwai wanda za ka gan shi cikakken Ustazu ne, ba shi da tsauri sam, idan ka hango sa cikin yara za ka rantse shi ma yaro ne, saboda hira sosai da yake yi da su. 


Wani ustazin gani na yi har tafawa suke yi, daga sun gan sa har rige-rige suke, shi kuma sai ya sakar musu murmushi ya tarbe su cikin nishaɗi. Wani har da 'yar tsaraba yake ba su, ba fa yaran gidansu ba ne, shi hakan yake wa duk yara. Ina ga 'ya'yansa?


Balle ka hango mu'amalarsa da ƙannansa kowa ba ya son ya yi nisa, sai dai ka ji ana ina wane? Mahaifiyarsa tana matuƙar son sa saboda yadda yake kyautata mata, mahaifinsa ma sanya masa albarka yake.


Idan ka gan sa cikin matansa kowacce kishin abin ta take, ba ta son ya mata nisa, idan tafiyar kwana kaɗan ta same ta sai ta ji kewarsa ta lulluɓeta ba ta samun sukuni sai ta lalubesa a wayarta, burinta ta faɗa masa ta yi kewarsa shi kuma ya rarrasheta, tana kewar yadda idan ta yi ko tari zai ce mata sannu, balle ta ce kanta na ciwo duk sai ya bi ya kiɗime.


A gaisuwa suna rige-rige tana ka bari na gaisheka, yana a'a bari na gaisheki dai ai ke Gimbiya ce, bai ankara ba sai dai ya ga ta zube a ƙasa, tana kwasar gaisuwa ba yadda ya iya zai ɗagota, yana murmushi yana sa mata albarka, zaman dai akwai garɗi.


A kasuwa ko wurin aiki ana girmamasa, kowa nasa ne ,yana umartar kowa da kyawawan aiki, idan ya ga ka yi kuskure sai ya kirawo ka, ya fara faɗa maka yadda kake da muhimmanci, sannan ya ce na yi mamaki da na ga kana abu kaza? Shin me ya sa ka yi ? Cikin mutuntawa za a yi a gama, nan take mutumin zai ji ya shiga zuciyarsa.


Me tsananin ibada ne ba ya son sallar jam'i ta wuce sa haka ma azkar, karatun Kur'ani, mai kamewa ne, mai umarni da kyakkyawa, mai hani ga mummuna, koda ya aikata mummuna zai roƙi Allah ya yafe masa, kuma zai yi ƙoƙarin kiyayewa.


Ba ya taka sutura, yana son tara gemu domin aiki da umarnin Annabi (S.A.W), da siffanta da mutanen ƙwarai, mai son tsafta ne, yana son nishaɗi lokaci zuwa lokaci domin wanke damuwar da take ƙunshe aran shi da mayar da komai ba komai ba.


Idan ba shi da aure mai kamewa ne, idan yana da 'yar budurwa mai gyara mata kurakurai ne, yana umartarta da zuwa Islamiyya,  karatun Kur'ani, sallah, azakar da ba ta shawarwari kan kulawa da kanta, ba ya nufar ta da alfasha ko ƙoƙarin koya mata, mai kyautata mata ne gwargwado, mai mantar da ita mayaudaran samari masu hure kunnen 'yan mata ne saboda shi ɗin maƙura ne wajen soyayya.


Ƙarshe


Wani zai ji akwai wasu ɗabi'un shi akwai kuma wasu ba nasa ba da sauransu, to kar ya damu, mu a wurin mu sunansa Ustazi.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.


Allah ya datar da mu kan daidai Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user