Wednesday, 27 November 2024

Tasirin Canje-canje Ga Rayuwar Ku

Tura Wannan Zuwa Ga

Yayin da muke girma muna ƙara fahimtar rayuwa. Muna tsintar kanmu cikin canje-canjen abubuwa game da ɗabi'a, tunani da yadda muke kallon duniya.


Tasirin canje-canje ga rayuwar ku
Hoto: Inc

Marubuci:- Abubakar S. Wali


Abin da muke ɓata lokaci a kansa yanzu ko kallo bai ishe mu ba, abin da yake ɗaukar hankalinmu a baya yanzu ya zama ba shi da wannan tasirin, abubuwan da muke ɗauka masu muhimmanci a baya yanzu sun rasa wannan ma'anar. Ra'ayoyinmu game da abubuwa daban-daban na rayuwa suna canzawa.


Haka zalika wannan canje-canjen na shekaru yana shafar har alaƙar mu da mutane amma ba mu fiye la'akari da hakan ba.


Misali


Abotar mu yanzu da wasu ba ta bada armashi kamar da, alaƙar mu ta yanzu da wasu ba ta bada ma'ana kamar da, amma saboda muna da ɗabi'a na maƙalewa abin da aka san mu da shi tun farko sai mu maƙalewa wannan mu'amalar koda kuwa a ce muna samun cutuwa ko muna cutar da wani a cikin mu'amalar, haka za mu ci-gaba da yin mu'amalar da daɗi ba daɗi, idan alaƙar ta haifar mana da damuwa mu zargi abokanmu ko mu zargi kanmu.


Manufa


Lokaci ba abin da yake bari, matuƙar kana rayuwa mai ma'ana za ka samu kanka kana girma a fanni daban-daban na rayuwarka. Wannan girman zai shafi hatta alaƙarka da mutane, saboda haka duk wata abota ko mu'amala ko alaƙar da ba za ta girma ko ta ci-gaba tare da kai ba babu amfani ka tsaya asarar lokaci da kuzari a kanta, maimakon haka ka ɗauki wannan lokaci da kuzarin ka zuba jarin su a cikin mu'amalar da take daidai da wajen da kake a rayuwa ko wajen da kake son zuwa.


Ba wai ka yanke mu'amala da wasu ko ka datse abota ake nufi ba, abin da ake nufi ka zuba lokacinka da kuzarinka a cikin alaƙar da ta dace da wane ne kai a yanzu.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user