Kamar yadda kowa ya sani, a kodayaushe, a komai ka sa gaba to ana tsammanin cewa za'a iya samun matsala, za'a iya samun ƙalubalen da zai sa ka ji cewa kamar ka sare, kamar ba za ka iya cimma burin ka ba. To amma kafin nan shin ko ka taɓa tunawa kan kanka cewa matsaloli da ƙalubale ba dawwamammun abubuwa ba ne, haka zalika nasara ita ma ba ta dawwama.
Marubuci:- Ibraheem Aleeyu
Shin ko ka taɓa tunanin yadda za ka juya matsalolin ka su zama nasara a maimakon faɗuwa?
Shin ko ka san da cewa tafiyar da ta ginu tun daga farkon ta har ƙarshen ta babu faɗuwa ba za ta zama kamar wadda a ka yi ta cike da ƙalubale ba?
Misali
Wani Sarki da ya mulki wani ɓangare mai yawa a duniya, ya fuskanci ƙalubale masu ɗimbin yawa, inda Sarkin da ya fi kowa aminta da shi a cikin sarakuna ya aiko masa da yaƙi domin cire shi daga kan mulkinsa, haɗamammen ɗan uwansa wanda suke gasa akan mulkin ya haɗa kai da wannan sarki, aka ƙwace duka dukiyarsa aka kuma kore shi, ya yi tafiya tun daga tsakiyar Asiya har Misra, da sauran ƙalubale da dama da ya fuskanta.
Sai dai kuma tarihi ya nuna cewa a ƙarshe waɗannan ƙalubale da ya fuskanta su ne suka zama tsanin nasarar sa, har ya zama ya dawo birnin sa, ya kuma karɓi mulkin birnin da birnin abokin nasa duka sun dawo ƙarƙashin sa, da ƙarin dabaru da ƙarfin da zai tunkari kowacce ƙasa kuma ya ci nasara a kanta, haka zalika da dabarun da zai kare ƙasar sa daga dukan mahara komai ƙarfin su komai yawansu, wanda kuma ba don wannan ƙalubalen da ya fuskanta ba da bai samu wannan nasarar ba. Wannan shi ne yadda ake juya matsala zuwa nasara.
Shin ko ka san cewa kai ma za ka iya mayar da matsalolin da ka fuskanta yayin ƙoƙarin cikar burin ka zuwa tsani na cimma nasarar ka sama da a ce ba ka fuskance su ba?
Wannan Sarkin da akwai wani rubutu da ya yi wanda shi ne ya dinga tunkuɗa shi har sai da ya ga cewa ya ci nasara, bai wuce layi biyar ba amma na san zai amfane ka wato cewa:
"Za'a iya samun cikas a ayyukan mu, amma ba za'a taɓa samun cikas a niyyar mu ba, saboda za mu iya komawa gefe mu jira har mu shirya, zuciya ta natsu sai kuma ta koma ga bigiren da ta baro wanda wani ƙalubale ya dakatar da mu"
Sannan ya ƙare da cewa:
"Samun cikas a aiki yana inganta aikin ne, haka zalika duk abinda ya tsaya a hanya shi ma ya zama hanyar".
Shin ko ka lura da darussan da ke cikin wannan zance?