Yau ma gani cikin fadarka ba na buƙatar komai sai kallon fuskarka don Allah ka amince na gano kyawunka. Godiya zan yi gare ka sarkin sarakuna mai farar zuciya ga ka da kyau kamar zinare dole ne na ce maka sarki.
Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR
Ladubban so da ƙauna sun samu masauki cikin soyayyar da aka ginata bisa tsarin gaskiya da amana, hakan ne dalilin da ya sa shaƙuwarmu da kai take ƙara nisan zango har muke saurin shallake masoya suke ƙoƙarin koyi da irin rayuwar soyayyarmu.
Na fahimci abubuwa na musamman a tare da kai. Ka haɗu kuma ka halittu, ka san so kuma ka san haƙƙoƙin ƙauna.
Ingantacciyar sallama daga ƙarƙashin inuwar ruhin zuciyar da ke yawan begenka a kullum.
Zuwa gare ka mashahurin masoyina wanda ya yi nasara wajen sace zuciyata.
Saƙon so na zo na ba ka don haka ga zuciyata nan ɗauki ka faɗawa gidanku zan zo da sadaki.
Ko ka san Allah ya halicceka cikin halittun da suka halittu wajen ƙawatuwar wannan duniya tamu?
Saduwar zuciyoyinmu wuri guda shi ne haɗuwar ruhinmu idan muka zamto cikin wannan yanayin dole ne mu dinga tunanin junanmu.