Babu abun da yake daƙushe baiwar mutum a rayuwa kamar ƙoƙarin mutum na zama wani daban saɓanin asalin yadda yake a halitta da fahimta. Babu abun da zai fito da baiwar ka a duniya kamar zamowa kai, ka zama kai ba wani daban ba.
Marubuci:- Abubakar S. Wali
Daga lokacin da ka tsinci kanka babu matsi na kwaikwayon rayuwar da ba taka ba daga lokacin ka samu wani ƙarfi/iko da zai ba ka 'yancin zama cikakken mutum.
Ga wasu abubuwa da za su taimaka maka wajen yin rayuwa a asalin yadda kake.
Sanin kai
Tasirin sanin kai da yin rayuwa daidai kai, a yadda kake.
Ba za ka iya zama kai ba sai ka san wane ne kai ɗin, ka san kanka, ka nazarci kanka kamar wani kake nazarta. Me kake so ? Ina ƙarfin ka yake? Ina raunin ka yake? Ina kake son zuwa? daga ina kake?
Rashin jin kunyar bayyana kai
Ya zama babu wani abu da kake ɓoyewa mutane game da asalin ka ko bayan ka. Ya zama mutane suna saurin sanin asalin ka idan suna mu'amala da kai ba dan nuna alfahari ba sai dan ba ka rufa-rufa ko ɓoye asalin ka.
Rashin tsoron bayyana ra'ayi ko fahimtar da ta saɓa da gama garin mutane
Hakan ba ya nufin ka yi ta hayaniya da mutane wajen bayyana wannan ra'ayin ko fahimtar, abun da ake nufi shi ne babu wani matsi daga mutane da zai sa ka yi wa kanka ƙarya ta hanyar bayyana ra'ayi ko fahimtar da ka san sun saɓa da naka. Ya zama ba ka damuwa akan ra'ayoyi da fahimtar mutane da suka saɓa da naka, sannan kuma ba ka damuwa da bayyana naka ra'ayi da fahimtar a duk lokacin da buƙatar hakan ta tashi.
Ka bar mutane su ma su zama su
Duk yadda ka kai da sanin kanka da yin rayuwar da ta dace da kai, ba za ka taɓa jin daɗi ba idan su ma mutanen ba ka musu wannan uzurin ba. Dole ka bar kowa ya yi rayuwa a yadda yake, kada ka yi ƙoƙarin canja mutane ko fatan mutane su zama wani abu daban, dole ka koyi karɓar mutane a yadda suke gaba ɗayan su, ka karɓe su da rayuwar su, da fahimtar su, da wautar su, da ilimin su, da jahilcin su.
Kada ka zama ɗan a bi Yarima a sha kiɗa
Ya zama kana da tsayayyen ra'ayin kanka akan kowane al'amari ba kawai inda aka fi yawa ko inda ya fi shahara kake bi ba. Ya zama ba wai ƙoƙarin bambanta kanka da mutane kake yi a kowane lokaci ba, a'a ya zama babu wani matsi da zai tilastaka yin abun da ya saɓa da fahimtar ka ko wane ne kai a mutum.
Rashin damuwa da tunanin mutane a kanka
Wannan kamata ya yi ya zama na farko saboda muhimmancin sa. Mutane da yawa, damuwa akan tunani ko ra'ayin mutane a kansu ya jefa rayuwar su cikin ƙunci.
Abun da ya kamata ka fahimta shi ne: mutane suna da dama ko 'yancin samun kowane irin tunani ko ra'ayi a kanka mai kyau ko mara kyau, ba ka da iko akan wannan, amma wannan ra'ayi ko tunanin nasu a kanka ba shi da tasirin cutar da kai.
Damuwa akan tunanin su a kanka shi ne abun da zai cutar da rayuwar ka, saboda haka wauta ne ka zama wani daban domin kawai wani ya samu tunani ko ra'ayi mai kyau a kanka.
Ka kasance a yadda kake.

