Showing posts sorted by relevance for query Abuna'Ila Saminu. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Abuna'Ila Saminu. Sort by date Show all posts

Friday, 12 July 2024

Rayuwa Da Abokai (2)

Rayuwa Da Abokai (2)

A kashin da ya gabata mun yi bayanin cewa, abokan mu'amalarka sun kasu uku: masoya, maƙiya da mahassada.


Mu'amala da abokai
Hoto: Telegraph


Marubuci:- Abuna'Ila Saminu


Mun kuma yi bayanin yadda kowanne kaso yake takunsa dangane da yin mu'amalarsa da kai.


A wannan kashin insha Allahu za mu yi bayanin dalilan da suke jawo samuwar kowanne ɗaya daga cikin abokan mu'amalar naka da muka zayyana, da ma yadda ya kamata ka yi wa kowanne ɗayansu mu'amala, idan matsayinsa ya bayyana gare ka.


DALILAI

Kowanne daga kason abokan nan naka akwai dalilin da ya sa ya zama yadda yake game da kai, kamar haka:-

MASOYI

Dalilin da yake kawo zama masoyi ya danganta da halin mutumin, da yanayin yadda ya fahimci mu'amalar da ka ke yi masa. Wani ya kan so ka ne saboda kyawawan halayenka, wani saboda siffar da Allah ya yi maka, wani kuma kawai gamon jini ne, sai ya ji ka kwanta masa a rai. Wannan shi ya sa maƙiyi na iya juyewa ya zama masoyi, saboda afkuwar ɗaya daga dalilan nan, musamman na ɗaya.


MAƘIYI 

Ƙiyayya na tasowa ne ta dalilin samun saɓani, ko mummunar/kuskuren fahimta, ko saboda waɗansu halayenka da ba su gamsar ba, ko kuma rashin haɗuwar jini. Wannan shi ya sa masoyi kan juye ya zama maƙiyi, domin wani dalili da ya taso daga waɗanda aka lissafa, musamman na 1, na 2 ko na 3.


MAHASSADI

Shi wannan yana faruwa ne sakamakon ɗaukaka ko wata baiwa da ya ga Allah ya yi maka, kamar kyawun halitta, ko ilmi, ko mulki, ko kuɗi, ko ka rabauta da abin da ku ke nema tare, sai shi kuma bai samu ba, ko ya ga mutane suna yaba maka, ko Allah ya ba ka karɓuwa wajen jama'a, ko ki samu mijin aure ita kuma tana kasuwa, da dai abubuwa masu kama da waɗannan. Daga dai zarar ya fara jin cewa shi ne ya fi ka cancanta da duk abubuwan da na zayyana maka.



A kashi na gaba, Insha Allahu, za mu yi bayanin yadda ya kamata ka yi wa kowanne daga cikinsu mu'amala. Idan har matsayinsa ya bayyana gare ka.

Tuesday, 10 March 2020

Ki Tambayi Kanki Wannan Tambayar Kafin Ki Fara Mu'amala da Dandalin Sada Zumunta

Ki Tambayi Kanki Wannan Tambayar Kafin Ki Fara Mu'amala da Dandalin Sada Zumunta

A yayin da kike ta baje kolin hotunanki a gayan naki a shafukan Social Networks, baya ga yabawar da shaiɗanun Bil Adama suke yi miki.

Ki Tambayi Kanki

Marubuci:- Sheikh Abuna'ila Saminu

Shin hakan ya sa kin samu masoyi/mijin aure, wanda da gaske ya ke?

Ko kin fahimci cewa da hotunaki na baya da suka gani, da na yanzu tsufanki suke baiyana wa masu gani? Idan har ba ki fahimci hakan ba, to ɗakko na shekaru biyu baya da kika saki, da kuma na kwanan nan, sai ki gwada ko za ki iya tantance hakan !

Kina zaton cewa duk masoyinki na gaskiya, wanda yake da kwaɗayin aurenki, zai kuma rinka jin daɗin ki barbaza hotunanki a yanar gizo-gizo, yana ganin ki a gayanki, shi da dukkan ma sauran abokanki/samarinki?
Idan har hakan ba ya damun sa, kin gamsu cewa son gaskiya, tsakani da Allah kuwa yake yi miki?

Kina ganin cewa namijin da yake son aurenki, rashin kishin da yake nuna miki, yana tabbatar miki da cewa yana kaunar ki?

Mai hankali shine wanda yakan yi nazarin ribar aikin da yakan yi, akai-akai !

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 14 July 2024

Rayuwa Da Abokai (3)

Rayuwa Da Abokai (3)

A kashi na biyu mun yi bayanin dalilan da suke samar da nau'o'in abokan alaƙarka guda uku. Yanzu kuma Insha Allahu, za mu yi bayani a kan yadda ya kamata ka yi wa kowanne daga cikinsu mu'amala, idan har matsayin su ya bayyana a gare ka.


Zama da abokai
Hoto: The tech edvocate


Marubuci:- Abuna'Ila Saminu


MASOYI

Ka riƙe shi kam, ka ci-gaba da yi masa abubuwan da suka sanya soyayyarka a zuciyarsa, ka ƙara fito da sababbin hanyoyin kyautata masa, ka riƙa yi masa kyakkyawar addu'a, da fatan alkhairi a duk wani abin da ya sa a gaba na rayuwa, ka mayar da farin cikinsa naka, haka ma baƙin cikinsa naka.

MAƘIYI

Ka yi ƙoƙarin kawar da saɓani ko rashin fahimtar da ya shiga tsakaninku, ta hanyar nuna masa kyawawan halayenka, ka nuna masa ƙauna da soyayya, ka riƙa shiga sabgoginsa na arziki, da yi masa jajen abu mara kyau da ya faru gare shi, idan kuma na gudunmawa ne ka ba shi iya ikon ka.

MAHASSADI

Ka nemi tsarin Allah daga sharrinsa, kada ka taɓa nuna masa cewa ka gano shi, kada ka rika nuna masa duk wata ƙaruwa/ɗaukaka taka, ka toshe masa hanyoyin samun labari game da yadda kake gudanar da rayuwarka, yi ƙoƙarin barin sa a cikin duhu game da hada-hadarka.

Ka riƙa rokon Allah ya yaye masa cutar da ke damun sa, domin ita hassada wata cutar zuciya ce da ba ka da maganinta, sai dai addu'a da neman tsari, duk kyautatawar da za ka yi wa mai yi maka ita, ba za ta taɓa canza zuciyarsa game da kai ba, sai dai kawai ka nemi Allah ya yi maka maganinsa.

KAMMALAWA

Ka sani cewa abokai biyu na iya canzawa, Masoyi da Maƙiyi, amm Mahassadi ba ya canzawa, kuma duk kirkin ka, duk nagartarka, ba ka isa ka ƙetare waɗannan nau'o'in abokan mu'amala guda ukun ba, domin duk abin da kake taƙama da shi na nagarta ba ka kai Manzo (S.A.W) ba, shi ma waɗannan abokan mu'amala ukun da su ya rayu!

Ina ga kuma irinmu 'yan rayuwar ƙarshen zamani ? Allah ka haɗa mu da abokan mu'amala nagari.

Domin samun cikakken bayani a kan hassada, ire-irenta, dalilanta, hukuncinta, hanyoyin rabuwa da ita da sauransu, karanta rubutun da muka yi game da HASSADA a wannan shafin.

'Yan uwa na bar ku lafiya cikin fatan alkhairi mai ɗorewa har abada!

Da fatan Allah ya yafe mana kura-kurenmu!

Wednesday, 8 April 2020

Matakan Da Mai Hassada Zai Bi Domin Rabuwa Da Ita

Matakan Da Mai Hassada Zai Bi Domin Rabuwa Da Ita

Saka tsoron Allah da kuma dangana.

Matakan Da Mai Hassada Zai Bi Domin Rabuwa Da Ita...

Marubuci:- Sheikh Abuna'ila Saminu

Kiyaye haƙƙoƙin wanda yake yiwa hassadar.

Kaucewa baiyana ƙiyayya ga wanda yake yiwa hassadar.

Ganewa cewa hassada cutuwa ce ga mai yinta a duniya da lahira.

Yawaita yabon wanda kake yi wa hassada da ƙoƙarin kyautata masa.

Yawaita yin sallama ga wanda kake yiwa hassada.

Nisantar halayen da suke kawo hassada kamar girman kai da jin isa.

Ƙoƙarin tsarkake ayyukansa na alkhairi ga Allah kaɗai ( Ikhlas ).

Yawaita karatun alkur`ani.

Tuna hisabi da azabar Allah.

Yawaita yin addu`a da sadaka.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 6 September 2024

Mafita A Soyayyar Shafukan Sada Zumunta

Mafita A Soyayyar Shafukan Sada Zumunta

Masoyan kafafen sada zumunta, duk wanda ya fahimci canjin ra'ayi daga wurin abokin soyayyar da suka ƙulla da nufin aure, to matakin farko ya warware abotar da suka ƙulla (unfriend), idan duk da haka bai samu nutsuwa a zuciyarsa ba, ya toshe kafar saduwarsu (block).


Soyayyar Shafukan Sada Zumunta
Hoto: Wfla


Marubuci:- Abuna'Ila Saminu


Kada ka taɓa bari yaudara ta saka maka damuwar da za ta shafi lafiyarka, ka fahimci cewa; babu wani ɗan adam ɗin da idan babu shi ba za ka rayu ba, kai kaɗai mahaifiyarka ta haife ka, a duniyar nan kuka haɗu bayan ka gama haɗa hankalinka, na mene ne za ka cusa wa zuciyarka damuwa don ka rasa abin da wataƙila hakan ne ya fi zama alkhairi ga kowannen ku? 


Ko tagwaye kuka zo duniya da mutum, dole ne da akwai ranar da za ku rabu, koda kuwa kuna cikin ƙoshin lafiya da lafiyayyen hankalinku, ballantana wanda kafar sada zumunta ce sanadin haɗuwarku.


Wannan fa ina magana ne da waɗanda suka ƙulla soyayyar tasu da nufin raya sunnar Manzo (S.A.W), ba masu kullawa da nufin shashanci ba.


Sunday, 5 April 2020

Matakan Da Wanda Ake Yiwa Hassada Yakamata Ya Dauka

Matakan Da Wanda Ake Yiwa Hassada Yakamata Ya Dauka

Komawa ga Allah da tuba daga dukkan zunuban da za su iya ɗora abokan gaba a kansa.

Hassada Mugun Ciwo...


Marubuci:- Sheikh Abuna'ila Saminu

Dogaro da Allah ( Tawakkali).

Neman tsari da Allah da karanta azkar da addu`o`in neman kariya waɗanda shari`a ta zo da su.

Roƙon Allah da ya kare ka daga sharrin mahassada.

Kamanta adalci ga mai yi maka hassada da kaucewa mayar masa da irin ɓatawar da yake yi maka.

Yiwa mai yi masa hassada kirki.

Yiwa kansa rukiyya ta maganin hassada.

Ɓoyewa mai maka hassada baiwar da Allah ya yi maka.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tuesday, 9 July 2024

Rayuwa Da Abokai (1)

Rayuwa Da Abokai (1)

Abu ɗaya za ka fahimta game da abokan mu'amalarka, sai ka hutar da ranka, ka kuma sha maganin zama da su.


Rayuwa da abokai
Hoto: Focus on the family


Marubuci:- Abuna'Ila Saminu


Abin kuwa shi ne; ka gane cewa sun kasu gida uku:-


1. Masoyi.

2. Maƙiyi.

3. Mahassadi.


FASHIN BAƘI:-


MASOYI


Shi wannan babu abin da yake yi maka fata illa ci-gaban rayuwarka, farin cikinka da kuma murna da duk abin alkhairin da ya shafe ka, yana taya ka murna, ya kuma taya ka baƙin ciki.


MAƘIYI 


Shi kuwa ba ya ƙaunar ka, ba abin da ya dame shi da kai, ko zancenka ba ya son ji, ba ya taya ka murna ko baƙin ciki, ya kan yi murna idan ya ji wani abin baƙin ciki ya same ka, ba ya son jin labarin abin farin cikin da ya same ka, yana kuma nuna maka gaba ƙarara, ba ya munafuntar ka ko kaɗan, domin ba ya gudun ka san ƙiyayyar da ya ke yi maka, ba kuma ya son kusantar duk wurin da ka ke.


MAHASSADI


Shi wannan ganin ƙyashi yake yi maka, ba ya taɓa son ci-gabanka, ba ya farin ciki da duk wata baiwa ko ni'imar da Allah ya yi maka, fatansa ya ga wannan baiwar ko ni'imar da aka yi maka ta gushe, koda kuwa ba za ta koma wurinsa ba, ba ya so ya ji ana yabon ka, ransa kan ɓaci idan ya ga ƙaruwarka, kullum yana cikin bibiyar lamarinka, yana kuma hanƙoron ya ga ya kusance ka, domin hakan ne zai ba shi damar sanin duk wani abu da ya shafe ka, amma kuma ba ya fitowa zahiri ya nuna maka a gabanka, ba kuma ya son ka gano matsayinsa game da kai, ko abubuwan da yake yi maka.


DUBA WANNAN: RAYUWA DA ABOKAI (2)


A kashi na gaba, Insha Allahu, za mu yi bayanin dalilan da suke jawo samuwar kowanne ɗaya daga cikin abokan mu'amalar nan naka, da ma yadda ya kamata ka yi wa kowanne ɗayansu mu'amala. Idan matsayinsa ya bayyana gare ka.