Showing posts sorted by relevance for query El-nass. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query El-nass. Sort by date Show all posts

Friday, 15 November 2024

Zazzafar Wasikar Soyayya Ga Nafisa

Zazzafar Wasikar Soyayya Ga Nafisa

Assalamu Alaikum Nafisa, ya kike ya harkokin soyayyarki suke? Ya gurin aikin ki? Ina fatan komai yana nan lafiya. Nafisat ki saka wannan a zuciyarki cewar soyayyata a gare ki ba ta da ranar ƙarewa domin kuwa kin gina soyayyarki ne a cikin zuciyata kuma na sallama miki dukkanin zuciyata.


Wasikar soyayya zuwa ga Nafisa
Hoto: Liubomyr Vorona/Dreams time 

Marubuci:- El-Nass


Na sha ganin mata a duniyar nan da suka shiga raina sosai har na furta musu kalmar soyayya amma ban san na yi kuskure ba sai da na haɗu da ke a lokacin na ji babu abin da nake so a duniya idan ba ke ba, kuma zan ci gaba da son ki har abada.


Sarauniyata babu wani abu da yake da muhimmanci a duk lokacin da ba ki tare da ni, Nafisat idan har ba na tare da ke komai nawa zai yamutse ne. Ke ce jin daɗina, ke ce farin cikina, sannan kuma ke ce komai nawa.


Nafisat, idan har ina tare da ke ina jin matuƙar farin ciki. Na yi matuƙar farin ciki da na same ki a matsayin sarauniyar zuciyata.


Kin sanya zuciyata ta zama ƙarfaffiya. Zan ci-gaba da son ki ne da ɗaukacin dukkanin zuciyata.


Ina son ki, daga masoyinki  El-Nass.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

Friday, 22 August 2025

Kalaman Soyayya Ga Budurwar Da Ra'ayin Ku Ya Zama Daya

Kalaman Soyayya Ga Budurwar Da Ra'ayin Ku Ya Zama Daya

Na ɗauki tsawon lokaci ina bincike har kawo yanzu domin samun wacce za mu yi rayuwar aure tare mu gudu tare mu tsira tare, amma wani lokaci sai na ga kamar ba zan samu mai irin ra'ayina ba, har sai da na haɗu da ke sannan na tabbatar burina ya cika.


Kalaman Soyayya Ga Budurwar Da Ra'ayin Ku Ya Zama Daya
Hoto:  People images - Yuri A/Shutte stock


Marubuci:- El-Nass


A lokacin da na fara ganin ki sai da numfashina ya ɗauke. A lokacin da kika fara min magana sai da tunanina ya ɗauke.


A lokacin ne idanuwana suka tabbatar min da cewa ba su taɓa ganin wani abu mai kyawun sura tamkar ki ba.


A gare ki duk na samu abubuwan da nake buƙata.

Tuesday, 17 December 2024

Gajerun Kalaman Hikima Na Rayuwa

Gajerun Kalaman Hikima Na Rayuwa

Abokina kada ka damu don ka rasa wanda zai kula da kai a rayuwa, domin mutane da dama sun kasa kulawa da kansu ma ballantana kuma har su kula da wani, kai dai kawai ka damu da kanka.


Gajerun kalaman hikima na rayuwa
Hoto: UCSF

Marubuci:- El-Nass


Mutanen kirki tamkar bishiyar mangwaro suke, a yayin da kake jifansa shi kuma a lokacin yake sako ma 'ya'yan shi masu zaƙi domin ka sha.


Kada ka zama mai ƙyashi da hassada ga samun wani, domin ba za ka mutu ba har sai ka samu duk abin da Allah ya yi nufi za ka samu a duniya.


Ba laifin ka ba ne ka zama mummuna ta fuskar halitta, ko ka zama talaka domin ba kai ka yi kanka ba, Allah ne ya so ya gan ka a haka amma laifin ka ne ka zama mai mummunan hali domin hali shi ne mutum.


Mace na iya yafe maka duk laifin da kai mata amma ban da laifi ɗaya wato shi ne laifin rashin ba ta kulawa ta fuskar soyayya.


Ni ma anan zan iya yafewa duk wanda ya yi mini laifi ta fuskar zamantakewa amma ban da cin amana.


Duk wanda ya ce zo mu zauna to masoyinka ne kada ka sake shi.


Kada ka damu don ka rasa wani abu mai kyau wanda kake so, sau da yawa sai ka rasa abu mai kyau sannan kake samun mafi kyau.


Ka zama mai ra'ayin kanka domin ka rayu a kan abinda kake so, idan har ka rayu akan ra'arin wani har ka mutu burinka ba zai cika ba domin kuwa ba ka rayu akan ra'ayinka ba.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.


Allah ka ba mu abokan zama na gari Amin.

Tuesday, 14 January 2025

Gajerun Sakonnin So Masu Dadi Ga Budurwa

Gajerun Sakonnin So Masu Dadi Ga Budurwa

Kowanne irin matsatsi zan shiga a rayuwata, ko yaya jama'a za su tsane ni ba zan daina son ki ba.


Gajerun Sakonnin So Masu Dadi Ga Budurwa
Hoto: Big stock photos

Marubuci:- El-Nass


A lokacin dana fara ganin ki, ji na yi wani abu yana shiga zuciyata, ya wuce can ciki, inda babu wadda ta taɓa zuwa kuma har abada babu wadda za ta sake zuwa.


Kamar yadda taurari ke yin haske gami da ƙyalli a sararin samaniya, to haka fuskarki take haske gami da ƙyalli a cikin zuciyata.


A dukkannin lokacin da zuciyata ta shiga cikin yanayin ƙunci, to ba abin da kan fitar da ita daga wannan yanayi face daɗaɗan kalaman ki masu sanyaya ruhi wanda ya fi busar sarewa daɗin sauraro.


Zan so a kodayaushe kuma a kowanne lokaci na kalle ki, domin kallon kyakkyawar fuskarki na haifar mini da kwanciyar hankali a cikin raina.

Wednesday, 13 November 2024

Zafafan Sakonnin Kewa A Tsakanin Masoya Biyu

Zafafan Sakonnin Kewa A Tsakanin Masoya Biyu

Budurwa


Zan iya manta komai amma ka sani ba zan iya manta ka ba, haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka ba, haƙiƙa daga jiya zuwa yau ina cikin ƙunci mara misaltuwa, baƙin ciki ya ziyarci zuciyata wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala. Idan har na ce zan iya na yi ƙarya domin ni kaɗai na san irin halin da nake ciki na rashin jin daɗin tafiyarka.


Saƙonnin kewa a tsakanin masoya
Hoto: Mom junction

Marubuci:- El-Nass


Zuciyata na tafasa har na kan ji tamkar na fashe da kuka, ka sani cewa wannan saƙon zuciyata na sanar da kai, hannu aikinsa rubutawa ba wai ina faɗa ne don tsari ko don ka ji daɗi ba.


Daga lokacin da ka haɗa yanaka-yanaka ka yi gaba ni ma daga wannan lokacin na tattara duk wata walwalata da farin cikina na ajjiye su a can gefe gurin da ba za su taɓa kusanto ni ba.


Don haka ina sanar da kai ban yi fushi da abin da ka aikata ba kuma ban turo maka saƙon don ka bar abin da kake ba, illa na turo maka don na ji laifin ba daga gare ni yake ba.


Ka kasance cikin farin ciki ka huta lafiya.


Saurayi

Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraro da duk wani haske, haske a idanuwana. Ina fatan dai ba fushi kike da ni ba?


Na gode da kulawa, amma  ina ga ba ki kai ni shiga kewa da zullumi ba, da ma an ce ba a sanin muhimmancin mutum sosai sai a lokacin da ya yi nisa da kai. Haƙiƙa jiya na ƙara gasgata wannan maganar, domin nisantar da na yi da ke na wuni ɗaya sai na ji kamar shekaru dubu ne.


Kin riga kin zama fatar jikina duk wanda ya raba ni da ke kamar ya raba ni da kyauna, kwarjinina haɗe da suturata ce.


Hasken zuciyata farin cikin raina, annashuwa da jin daɗina. Ina sonki ina ƙaunar ki, ba zan iya nisa da ke ba. Ba zan bar ki ba duk rintsi duk wuya, sai dai idan ke ce kika bar ni  zuciya kuwa ba ta fatan ko mafarkin hakan balle a gaske.


Ina so ki sani cewa soyayyarki ta yi nisa a cikin zuciyata.


Ke garkuwa ce a gare ni mai kare ni daga abubuwa da dama.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

Sunday, 17 November 2024

Zafafan Gajerun Sakonnin Kauna Na Soyayya

Zafafan Gajerun Sakonnin Kauna Na Soyayya

Zuciyata akan ƙaunarki ba za ta taɓa karaya ba, murmushina ba zai taɓa tsufa ba, soyayyar mu da ke ba ta da iyaka ina matuƙar ƙaunarki.


Gajerun Saƙonnin Ƙauna Na Soyayya
Hoto: Aecc global

Marubuci:- El-Nass


Idan da za a ce na zaɓi matar da nake so na aura mu yi ta zaman aure har mutuwa, da sai na yi amfani da damata ta ƙarshe na ce miki ke ce zaɓina na har abada.


Kasacewata cikin nutsuwa shi ne na kasance tare da ke a cikin rayuwata, soyayyar ki a gare ni tamkar ruwan sha ne da nake sha a kullum a duk bayan wasu daƙiƙu.


Idan a ce ina da zabi akan soyayyarki da kuma numfashina tabbas zan yi amfani da numfashina na ƙarshe na ce miki ina son ki.


Rayuwata tana cikin ruɗu idan na wayi gari ban saki a cikin idanuwana ba.


Zuciyata ba za ta iya jure zaman kaɗaici ba idan har ba ta tare da ke.


Idan na kalle ki sai na ga tamkar babu kyakkyawa kamar ki saboda haka nake gode wa Allah da na same ki a matsayin masoyiyata ta har abada.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

Sunday, 8 December 2024

Zafafan Kalaman Kiran Waya Ga Budurwa

Zafafan Kalaman Kiran Waya Ga Budurwa

Lallai ba shakka son ki zai iya zama ajalina, musamman idan zuciya ta rasa ki babu makawa zan bar duniya da zanen hotonki a bangon zuciyata.


Zafafan Kalaman Kiran Waya Ga Budurwa
Hoto: Royalvectors/Vecteezy

Marubuci:- El-Nass


Kin shiga raina cikin rashin zato ko tsammanin zuciya, sakamakon damuwar rashin ki da ke cikinta ta zamo jigon da zai iya kai ta ga halaka.


A kullum sauraren sautin muryarki ne yake ƙara jefa ni cikin nishaɗi da farin ciki, domin na riƙe ki a matsayin makamin da zan yi yaƙi da shi a cikin duniyar masoya.


Komai rintsi komai wuya ba zan furta da-na-sanin soyayyata da ke ba domin na kan samun rahotan zato da tsammanin cewa soyayyata da ke alkhairi ce.


Ganin kyakkyawar fuskarki kan iya samar mini da warakar damuwa da baƙin cikin zuciya.


Ki yarda da cewa ina sonki. Kuma ba zan sauya ra'ayina ba koda so da ƙauna za su zama matsala a gare ni, ke ce ɗaya tilo.


A halin yanzu idan na rasa rayuwata son ki shi ne sanadi domin ina da tabbacin cewa girman soyayyarki zai iya haddasa mutuwar da za ta zama tarihi a cikin fadar masoyan asali.


Rayuwata da dukkan darasin da ke cikin ta suna a gare ki mallakar ki ce. Fatana ki riƙe ni amana.


Kyakkyawan lafazin bakin ki shi ne linzamin da ke janye ra'ayina wajen sha'awar zama kusa da wata 'ya mace.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

Thursday, 12 December 2024

Gajerun Kalamai Masu Dadi Ga Budurwa Na Soyayya

Gajerun Kalamai Masu Dadi Ga Budurwa Na Soyayya

Da ma a ce ina da damar da zan iya buɗe miki zuciyata, da tabbas kin ga yadda na cika ta da sunayen ki wanda hakan ke nuna cewa ba zan taɓa rabuwa da ke ba.


Gajerun Kalamai Masu Daɗi Ga Budurwa Na Soyayya
Hoto: Zero creative/Getty Images

Marubuci:- El-Nass


Ki yi sani sani cewa a duk lokacin da ba ki a kusa da ni tamkar bishiyar da take rayuwa ne ba tare da hasken rana ba.


Murmushin ki shi ne farin cikin zuciyata. Kukan ki shi ne baƙin cikin zuciyata. A kusa ko a nesa ba zan taɓa mantawa da ke ba.


Ban taɓa jin son wani abu a rayuwata ba tamkar ki ba, sannan ba zan taɓa ƙaunar wani abu ko wata mace tamkar ki ba. Ina fatan ke ma haka nake a wajen ki?

Monday, 25 November 2024

Gajerun Sakonnin Soyayya Na Safe

Gajerun Sakonnin Soyayya Na Safe

Soyayyarki ta zame mini tamkar inuwar jikina, duk wani motsi da zan yi to na kan yi ne tare da ita.


Gajerun Saƙonnin Soyayya Na Safe
Hoto: Vecteezy

Marubuci:- El-Nass


Kowacce rayuwa akwai wani abu mafi amfani a cikinta, abu mafi amfani a rayuwata shi ne soyayyarki.


Taswairar fuskarki ce ke bayyana a duk lokacin da na dubi zoben da ke hannuwana.


Ƙadangare kan samu shiga cikin bango a yayin da bangon ya tsage. To haka soyayyarki ta samu shiga cikin zuciyata a yayin da kika samu makullin zuciyar tawa.


Ba na tunanin rayuwa tana iya gudana idan har babu ruwa gami da iska, haka jin daɗi gami da walwala ba za su tabbata a gare ni ba, idan har ba tare da ƙaunarki ba.


Soyayyarki ce babban sinadarin da ke sarrafa zuciyata.


A kowacce rana na kan ji farashin soyayyarki na ƙara hauhawa cikin zuciyata, ke ce mafi cancanta da jan ragamar rayuwata. Ina sonki a kowanne irin yanayi.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

Wednesday, 20 November 2024

Zafafan Kalaman Soyayya Na Hausa

Zafafan Kalaman Soyayya Na Hausa

Minti ɗaya tare da ke kamar wani ɓangare ne a aljannar duniya, duk lokacin da muke tare lokaci na tafiya da sauri, ina matukar son kasancewa tare da ke ya sahibata.


Zafafan Kalaman Soyayya Na Hausa
Hoto: Dreams time

Marubuci:- El-Nass


Idan kika tsinci murmushin da ba ki san dalilin shi ba, kar ki damu ina tunaninki ne a lokacin kuma ina murmushin ni ma.


Idan ina cikin rayuwar ƙunci na gwammace na gan ki fiye da samun tufa zazzaƙa.


Kalma ɗaya ce ta kuɓutar da ni daga duk wani nauyi da ciwon rayuwa, wannan kalmar kuwa ita ce so, har yanzu ina son ki ya sahibata.


A rayuwa na koyi soyayya, murmushi, farin ciki da zama jarumi mai gaskiya, na koyi yadda zan zama mai imani mai yafewa, amma har yanzu ban koyi yadda zan iya mantawa da ke ba.

Monday, 18 November 2024

Gajerun Sakonnin Soyayya Na Dare

Gajerun Sakonnin Soyayya Na Dare

Soyayyar ki tana ɗawainiya da rayuwata, ta gama ratsan zuciya. Ya abar sona ke kaɗai zan yi wa kwalliya, domin na san na dace da samun ɗiya mai tarbiyya, mai kyawun tafiya, ina ƙara tabbatar miki a duk sa'adda kika yi sassanyar dariyarki sai ƙaunarki ta ƙara ninkuwa a zuciyata.


Gajerun Sakonnin Soyayya Na Dare
Hoto: Stock adbobe

Marubuci:- El-Nass


Masoyiya, ba na tunani, kuma ban taɓa kawo a raina cewa soyayyarki za ta taɓa gushewa daga zuciyata ba, kamar yadda na yi imanin falwaya ba za ta taɓa fitar da ganye ba, kamar yadda cewa ba za a taɓa samun jaki mai kaho ba.


Ina matuƙar girmama soyayya a rayuwata a saboda ke.


Duniyar soyayya wata duniya ce mai cike da farin ciki da sanya shauƙi a zukata, na shiga wannan duniyar ba na fatan fitowa daga cikinta, na san ma ba za ki taɓa bai wa wani ƙofar da zai shiga cikin ta ba balle ya takura mini har ya yi yunƙurin fito da ni.


So tamkar mikiya yake, yana ɗawainiya da zuciya, fatana na riski babban burina wato na mallakeki a matsayin mata a gare ni, uwar 'ya'yana mai tarairaya da ba ni farin cikin rayuwa.

Tuesday, 12 November 2024

Zafafan Sakonnin Kwanciya Bacci Na Soyayya

Zafafan Sakonnin Kwanciya Bacci Na Soyayya

Ina so na kwanta na yi bacci yanzu amma na kasa, kin san mene ne ya sa? Saboda tunanin ki ba zai bar ni na yi ba. Na rasa yadda zan yi da rayuwata saboda kowanne lokaci ƙwaƙwalwata tana cikin zunzurutun tunanin ki ne. Da fatan dai ke ma kina jin abin da nake ji a kanki?


Saƙonnin kwanciya bacci na soyayya
Hoto: Space talk

Marubuci:- El-Nass


Na bincika zuciyata ciki da waje amma na rasa abinda nake ƙauna kuma zan ci-gaba da ƙauna har ƙarshen rayuwata idan ba ke ba.


Ina ƙaunar budurwa rantsattsiya ta ko'ina kamar ilimi, hankali, nutsuwa, tarbiyya da addini, iya kwalliya sannan da iya soyayya, a gare ki duk na samu waɗannan abubuwan da nake buƙata.


Ina so na zauna na ci abinci yanzu amma na kasa, kin san mene ya sa? A duk lokacin da na ɗauki kwanon abincin hoton ki nake gani kina mini murmushi.


Ke ce tauraruwa mai haskawa, na san ba za ki taɓa koɗewa ba, za ki zama fitila wacce za ta taimaka min na karanta taswirar zuciyata.


Rayuwata tana cikin ruɗani idan na wayi gari ban saki a idanuwana ba, zuciyata ba za ta iya jure zaman kaɗaici ba idan har ba ta tarar da ke ba, don Allah kada ki yi nisa da ni.


Ina matuƙar girmama soyayya a rayuwata, duniyar soyayya wata duniya ce mai cike da farin ciki da sanya shauƙi a zukata, na shiga wannan duniyar saboda ke ba na fatan fitowa daga cikin ta har abada.


Idan mutane goma suka kula da ke, ɗaya daga cikin su ni ne. Idan mutum ɗaya ya kula da ke, shi ma ni ne. Idan kuma babu wanda ya kula da ke, wannan yana nufin ba na cikin duniyar nan a raye.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.