Showing posts sorted by relevance for query Rabs. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Rabs. Sort by date Show all posts

Friday, 29 November 2024

Sakon Zuciya Ga Masoyiya

Sakon Zuciya Ga Masoyiya

Ke ce farin cikina da annashuwata. Ina nan riƙe da amanar son ki har ƙarshen rayuwata, ba zan taɓa bai wa kowa ba sai ke kaɗai.


Saƙon zuciya ga masoyiya
Hoto: Marriage

Marubuci:- Rabs


Masoyiya, son ki a gare ni tamkar wani kyakykyawan fure ne da idanuwana ke fara ƙawatuwa da duban shi, hanci ya ji daddaɗan ƙamshin shi, ruhi ya yaba rai ya aminta.


Aminci ya tabbata a gare ki mai sona, ina son ki kamar yadda kike sona, ina tare da ke a kowanne yanayi domin kina kyautatawa zuciyata, kina ba ta farin ciki, duban ki kan kauda lalaci, sanadin son ki rayuwata ta sauya.

Sunday, 1 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Na Saida Safe

Gajerun Kalaman Soyayya Na Saida Safe

Kallon kyakykyawar fuskarki mai cike da annushuwa ya kan ƙaramin ƙarfin gwiwa da jarumtar da za su sa na ji kamar zan iya yaƙar duniya.


Gajerun Kalaman Soyayya Na Saida Safe
Hoto: Wallup

Marubuci:- Rabs


Kin kasance tamkar dukkanin wani motsina, a kullum idan ban saki a idona ba sai na kasance tamkar mara lafiya. 


Soyayyarki ruwan zuma ce a gare ni da zan sha domin warkar mini da wata cuta.


Zuciyata tamkar wani fage ne da yake cike da soyayyarki, na kasance a kullum ba ni da wani abu muhimmi wanda ya wuce tunaninki. Ina son ki rayuwata, ruhina, muradina, murmushina saida safe tawan.

Saturday, 16 November 2024

Kalaman Kewar Masoyi A Lokacin Da Aka Tafi Makaranta Zuwa Ga Habib

Kalaman Kewar Masoyi A Lokacin Da Aka Tafi Makaranta Zuwa Ga Habib

A duk lokacin da na buɗe idanuwana babu wanda nake fara gani sai kai Habib, na je makaranta amma na kasa zama saboda tsananin tunaninka da ya shige mini zuciya Habib.


Kalaman Kewar Masoyi
Hoto: Yaba compus

Marubuci:- Rabs


Burina ba zai kammala cika ba har sai na tabbatar mizanin soyayyata da taka sun yi kunnan doki kuma ba zan taɓa gazawa ba Habib har sai burina ya cika.


Me kake so na dafa maka ka ci yanzu kawai a matsayin kyauta?


Na gode maka da ka kasance a cikin rayuwata saboda ba ni da wani buri face na samu abokin rayuwa kuma na samu, sannan zan ci gaba da ƙoƙarin ganin na ci-gaba da rura wutar soyayyata a cikin zuciyarka.


Tabbas ire-iren waɗannan kalamai su suke zautar da mutum a yayinda budurwasa take sambaɗo masa su har ya zauce ya dinga kiran wayyo duniyata.


Da fatan 'yammatan wannan shafi za ku ƙara  dagewa wajen kulawa da masoyanku ta hanyar faranta musu zuciya?

Friday, 22 November 2024

Zafafan Kalaman Soyayya 3 Masu Kwantar Da Hankalin Saurayi Da Budurwa

Zafafan Kalaman Soyayya 3 Masu Kwantar Da Hankalin Saurayi Da Budurwa

Sirrance kalaman masoyi sukan ƙarawa soyayya lokaci sosai, daga bisani ma ta zama ta har abada, ya zama dole ki ɗauki kalaman masoyinki ki kai su wata mihimmiyar farfajiya ko fada a cikin zuciyarki.


Zafafan Kalaman Soyayya 3 Masu Kwantar Da Hankalin Saurayi Da Budurwa
Hoto: Freepik

Marubuci:- Rabs


1. Kin zamo tamkar jinin jikina a kowane lokaci, a kowacce daƙika jinina yake motsawa haka zalika ke ma a duk wannan lokutan kike motsawa a cikin jikina, raba ni da ke daidai yake da zuƙe jinin jikina.


2. Murmushinki ya kan jefa ni a cikin wani yanayi da nake rasa gane a duniyar wata nake ko a duniyar rana? Babu wanda zai gane sai ni kaɗai na gane a duniyar san ki nake.


3. Zuciyarki tamkar ɗanyen ƙwai ne wanda fashewarsa zai sa a yi asarar ruwan ƙwan da yake ciki ya zama dole na hankalta na nutsu na ci-gaba da kula da wannan ƙwai idan har ina so na ci-gaba da numfashi a doran ƙasa domin rayuwata babu ke mutuwa ce maganinta.


Daɗaɗan kalamai na ƙarawa zuciya ƙarfin gwiwa wajen gabatar da soyayya cikin nishadi da kwanciyar hankali ba tare da saɓawa ta shigo tsakanin saurayi da budurwa ba.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi a kyauta kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.