Showing posts sorted by relevance for query Yaron MLM KD. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Yaron MLM KD. Sort by date Show all posts

Wednesday, 13 November 2024

Sakon Budurwa Mai Sanyaya Zuciya Ga Saurayi

Sakon Budurwa Mai Sanyaya Zuciya Ga Saurayi

Amincin Allah ya tabbata a gare ka masoyina, kuma abin alfaharina, samun ka a rayuwata babbar nasara ce, ganin ka a kusa da ni ke saka ni annashuwa.


Sakon Budurwa Mai Sanyaya Zuciya Ga Saurayi
Hoto: Dreams time

Marubuci:- Yaron MLM KD


Kai nake fata a matsayin uban 'ya'yana, ni taka ce, kuma zan ci-gaba da ƙaunarka har ƙarshen rayuwata.


Tunanin ka nake a kodayaushe koda a cikin baccina.


Haƙiƙa na fi kowace mace sa'a domin kai mallakina ne, ka riga ka mamaye zuciyata da dukkanin sassan jikina. Kai ne zuciyata!

Friday, 17 January 2025

Kalaman Soyayya A Tsakanin Talaka Da 'Yar Mai Kudi

Kalaman Soyayya A Tsakanin Talaka Da 'Yar Mai Kudi

Haƙiƙa kin iya kallon soyayya domin kyakkyawan kallon ƙaunar da kike turo saƙonsa zuwa gare ni shi ne silar tabbatuwar cewa a fagen iya soyayya ba kowa ba ce kamar ki gwanata.


Kalaman Soyayya A Tsakanin Talaka Da 'Yar Mai Kuɗi
Hoto: Ofh soup kitchen

Marubuci:- Yaron MLM KD


Hmm na kan yi murmushi yayinda idanuwana su kai tozali da abin da kowacce idaniya ke buƙatar gani wato kyakkyawar halitta irin taki.


Yayin da zuciyata ta taho zuwa ga kyakkyawar sarauniyar zinariya, kuma me kyakkyawan takun ƙasaita fiye da na ƙananun sarakai.


Haƙiƙa tarayyata da ke ita ce kyakkyawar rayuwar da nake mafarki a kodayaushe masoyiya.


Duk da na kasance ba kowa ba amma na kan ji ƙwarin gwiwa ta ya ƙaru a duk lokacin da na gan ki a gefena.

Sunday, 15 December 2024

Lafiyayyun Gajerun Sakonnin Barka Da Safiya Ga Budurwa

Lafiyayyun Gajerun Sakonnin Barka Da Safiya Ga Budurwa

Safiya mafarin dukkan wuni. Ina fatan kin wayi gari lafiya tsokar jikina, duk da na san mun zanta kafin hakan, amma abun ka da mai ƙaunar ka sai ya ƙara jaddada hakan idan zuciyar ta motsa, Zainab ina ƙaunar ki ƙauna mai cike da girmamawa da kulawa.


Lafiyayyun Gajerun Sakonnin Barka Da Safiya Ga Budurwa
Hoto: Star 999

Marubuci:- Yaron MLM KD


Ba na tunawa da ko ranar haihuwata ko kuma ranar kammala karatuna domin har yanzu da sauran na yi farin ciki, ranar bikin mu ita ce ranar haifata kuma ita ce ranar kammala ɗan ilimin da nake nema. Allah ya faranta miki ƙanwata koda ni na gaza. 


Karramawa da aminci, gami da kuma tausayawa nake miki. Ina fatan hakan ya ɗore har zuwa lokacin da za mu koma ga mahaliccin mu mu yi rayuwar 'yanci, sahibata wallahi ƙaunar da nake miki sunan ta ya fi ƙarfin na kira ta da so sai dai na ce mata kankat.


Ranar auren ki ta zama kamar ranar samun 'yanci ce gare ni. Ina ƙaunar ki matuƙa mu wuni lafiya. Bissalam.


Daga naku Sarkin Masoya. Ku ci-gaba da kasancewa tare da ni a kullum a wannan shafin.

Wednesday, 30 October 2024

Gajeriyar Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Budurwa

Gajeriyar Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Budurwa

Haƙiƙa wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ce a taƙaice izuwa gare ki msoyiyata domin ki san cewa ke ce haske mafi annuri a cikin zuciya da ruhina baki-ɗaya, shiyasa nake son sanar da ke cewa samun amincewar saƙona a gare ki shi ne mahaɗin cikon farin ciki da kuma wanzuwar hasken ƙalbina.


Gajeriyar buɗaɗɗiyar wasiƙa
Hoto: Ace money transfer


Marubuci:- Yaron MLM KD


Ina fatan furucina na farko a gare ki ya kasance kamar haka, amincin Allah ya tabbata ga tabbatacciyar kyakkywar da kewarta ta zamo min jiki a duk lakacin da ba ta kusa da ni, bi ma'ana sarauniyar da na yarda da kyakkywar niyyarta ta bada kulawarta a gare ni wato ke kenan abar ƙauna kuma mahaɗin bugun zuciyata.


Zan kasance mai sauraron haka daga gare ki domin umarnin zuciyata ne. Sai anjima!

Saturday, 23 November 2024

Zazzafan Kalaman Yaba Kyautar Masoyi Daga Masoyiya

Zazzafan Kalaman Yaba Kyautar Masoyi Daga Masoyiya

Na karɓi kyautar zobe daga hannuwanka, kyautar tana alamta min kai ne wanda nake so, zobenka zai zama wakili na musamman a wajena domin kuwa duk lokacin da na kalle shi zan tuno da kai. Ina fatan ni ma nawa zoben zai zama wakilina a wajenka.


Zazzafan Kalaman Yaba Kyautar Masoyi Daga Masoyiya
Hoto: Brombergs

Marubuci:- Yaron MLM KD


Tabbas ina son ka a cikin raina.


Kai kaɗai kake ɗebe min kewa, idan na ji muryarka, na kuma ga fuskarka.


Ka kewaye dukkan zuciyata gami da ruhina.


Ka buɗe min zuciyarka tare da barka, na shiga cikin ta ta zamo sirrina.


Son ka shi ne komai a gare ni.


Muradina gare ka shi ne ka zamo uban

yarana. Kai nake ƙauna.


Na sallama maka zuciyata gami da ruhina.


Daga gwanin ku Sarkin Masoya.

Tuesday, 31 December 2024

Kalaman Soyayya Na Asuba

Kalaman Soyayya Na Asuba

Ke ce azancin kowanne bigiren hasken da yake ƙara haskaka fadar duniyar masoya, ra'ayina ne kallonki haka zalika ra'ayin kowa ne begenki domin kin cancanta kuma kin dace a daidaita kowanne harafin kalmomi da ambaton kyakkyawar surarki.


Kalaman soyayya na asuba
Hoto: Pinterest

Marubuci:- Yaron MLM KD


Da ke zan shiga taron gudanar da soyayyar gaskiya domin  gabatar da kowanne harafin annurin da yake cikin hasken kyawawan idanuwanki.


Ke ce sarauniyar da nake kishi.


Ke ce tauraruwar cikin ƙalbina.


Ke ce zinariyar da nake tattali da kulawa.


Ke ce kyakkyawar da nake alfahari da ita.


Ke ce autar da ke cikin fadar zuciyata.


Ke ce sinadarin hasken idanuwana.


Sha bege da kirari a cikin kalamaina.


Ke ce kowanne nau'in farin cikina.


Ke ce ma'abociyar kowanne murmushina.


Ke kika zamo jigon nishaɗina a soyayya.


Da ke zan kasance a kowane yanayi.


Farkon kallon da na yi miki shi ne cikakken bayanin shigowarki a cikin ƙalbina. Asalin kyawunki gami da haskenki shi ne lantarkin kyakkyawar kwalliyar da take bayyana annurin idanuwanki.


Tsarin sautin amon tattausar muryarki ya zarce ayarin kalmomin lafazin da zan iya furtawa ma'abocin sauraro, diri da haibarki su ne misalin kamannin kyakkyawar Gimbiyar da za'a kirata Sarauniyar masarautar birni da karkara.

Thursday, 14 November 2024

Zahirin Tsantsar Yadda Ake Yin Shagwaba A Aikace

Zahirin Tsantsar Yadda Ake Yin Shagwaba A Aikace

Shagwaɓa, da farko sai ki buɗe kunnen ki idan kuna kwance zai tashi ki fara kuka, kina shagwaɓa uhmmm uhmmm idan ya ce "Lafiya?" Ki ce masa ba kai ne ba, zai ce "Me na yi?". Sai ki ce "Gani na yi za ka cire min bargon da na rufe jikina da shi kuma sanyi nake ji". Zai ce "Ai ban cire ba". Ke kuma sai ki ce "Ai ɗumin jikinka ne bargon, ni ba wannan ba kawai ka dawo".


Zahirin tsantsar yadda ake yin shagwaɓa a aikace
Hoto: Deposit photos

Marubuci:- Yaron MLM KD


Kuna zaune ki ce "Baby zan sha ice cream". Idan ya ce "A ina zan samu ice cream yanzu?".  


Sai ki kalle shi cikin ido ki ce "Ba gashi nan ba". idan ya ce "A ina kenan?".


Sai ki ce "A bakinka". Sai ki yi masa French Kiss, ki ce "Ai yawun bakinka ya fi ice cream ɗin ma daɗi".


Idan kin shiga banɗaki kina wanka sai ki leƙo ki yi ƙara ki ce "Wayyo Baby".


Zai taho ya ce "Lafiya?".


Sai ki ce "Soson da zafi".


Zai ce "To ya za a yi?"


Sai ki ce "Ka shafa sabulun a hannunka ka yi min da shi zai fi soson daɗi, ba zan ji zafi ba".


Idan yana zaune a falo yana kallo, sai ki taso daga inda kike ki faɗa jikinsa, ki fara kuka idan ya tambaye ki, sai ki ce "Uhmm! Uhmm! Abin ƙauna ni kallo zan yi".


Sai ki yi kwanciyar ki a jikin shi.


Za mu ci-gaba Insha Allah.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

Tuesday, 26 November 2024

Sabon Gajeren Sakon Begen Saurayi Mai Zafi

Sabon Gajeren Sakon Begen Saurayi Mai Zafi

Aminci ya ƙara tabbata ga kyakkyawar halittar da babu irin ta a cikin idanuwana, tunanin ka nake a kullum, begen ka nake kullum, tunaninka shi ne abokin hira ta a kodayaushe domin kuwa muryarka ta fi siga da zuma zaƙi a gurina.


Sabon Gajeren Saƙon Begen Saurayi Mai Zafi
Hoto: Pinterest

Marubuci:- Yaron MLM KD


Kai ne abin sona domin kuwa kai nake so, kai ne masoyina domin kuwa kai ne uban 'ya'yana.


Kai ne my heart domin kuwa zuciyata tana hannunka.

Monday, 11 November 2024

Gajeriyar Wasikar Barka Da Safiya Ga Budurwa

Gajeriyar Wasikar Barka Da Safiya Ga Budurwa

A cikin salo na turo saƙona izuwa gare ki mai ɗauke da amintattaciyar sallama kamar haka, Assalamu Alaiki yake mai ado da kyakyawar siffa ta alfarma, ke ce nake miki laƙabi da tauraruwa mafi harke.

   

Gajeriyar wasiƙar barka da safiya zuwa ga budurwa
Hoto: Freepik

Marubuci:- Yaron MLM KD


To me zai hana ni ma turo miki ingantacciyar wasiƙar barka da safiya? Zan so ki sani cewa matsuwa gami da damuwa da damuwar ki ne ya sa nake son jin amsar kin tashi lafiya masoyiyata, domin amsar da za ki ba ni ita ce ginshiƙi kuma silar turo saƙon barka da safiya a gare ki abar ƙaunata.


Hmm silar wanzuwar farin cikina, sanadin ƙaruwar ƙaunarki ne ya sa na saki a farkon lissafina tun kafin a je ko'ina a cikin wannan kyakkyawar safiya ta yau abar ƙaunar farin cikin zuciyata, damuwar sanin kin tashi a cikin ƙoshin lafiya zai zamo silar farin cikina na wannan rana.

Sunday, 20 October 2024

Kyakkyawan Gajeren Sakon Barka Da Safiya Ga Masoyiya

Kyakkyawan Gajeren Sakon Barka Da Safiya Ga Masoyiya

Assalamu alaiki ya ke wannar kyakkyawar da zuciyata ke bugawa da haruffan sunanta, kamar yadda kika sani cewa daidaiton kowacce gangar jiki a haɗa ta da ruhin ta to haka ni ma mahaɗin nawa farin cikin shi ne jin kyakkyawar amsar da za ta sanya annuri a cikin zuciyata saboda ke.



Gajeren Sakon Barka Da Safiya Ga Masoya
Hoto: Wallpapers


Marubuci:- Yaron MLM KD


Idan har yaƙinina ya zamto gaskiya a gare ki cewa kin tashi lafiya kamar yadda ni ma na tashi lafiya. To zan kasance mai matuƙar farin ciki da shauƙi na musamman.


Karɓuwar saƙona a gare ki shi ne karsashin da zuciyata za ta samu kamar yadda nake ji a sanadin ƙaunarki. 


BARKA DA SAFIYA masoyiyata, abar ƙauna, shalelena, hubbina, sahibata, nurul ƙalbina, matata, farin cikina da annashuwata da  shauƙina.

Thursday, 26 December 2024

Gajerun Kalaman Nuna Tsantsar Kauna Ga Masoyiya

Gajerun Kalaman Nuna Tsantsar Kauna Ga Masoyiya

A kan son ki na shirya tsaf domin na sadaukar da jarumar zuciyata wajen yaƙi da masu nuna ƙiyayya a gare ki koda kuwa hakan zai sa na rasa rayuwata a sanadin ki.


Gajerun Kalaman Nuna Tsantsar Kauna Ga Masoyiya
Hoto: Deposit photos

Marubuci:- Yaron MLM KD


Uhmm Baby ina son ki fa. A duniyata babu kamar ki. A rayuwata babu tamkarki. Ki mallaka mini duniyarki.


Ina kokwanto cewa kina sona. Kyakkyawata mashahuriyata wasu lokutan ina ƙare nazarina a ta yaya ne zan tsaraki? Ta yaya zan saki nishaɗi? Ta yaya zan gusar da baƙin ciki a rayuwarki ? Ina burin na shahara a cikin hamshaƙiyar fadar ki Babyna.


Soyayyarki mai asalin samun asali ce wadda farkon asalinta yake faruwa a cikin iskar da nake shaƙa ina kai wa zuciyata shi ya sa na yi nisa cikin duniyar begen ki.

Monday, 23 December 2024

Zafafan Kalaman Soyayya Na Text Message Ga Budurwa

Zafafan Kalaman Soyayya Na Text Message Ga Budurwa

Ƙaunarki ce mafari kuma silar wanzuwar duk wani farin ciki ko haske a cikin duniyata, domin annurin amintacciyar zuciyarki ne mahaɗi ko na ce cikon farin cikin zuciyata a koyaushe.


Zafafan Kalaman Soyayya Na Text Message Ga Budurwa
Hoto: Adobe Stock

Marubuci:- Yaron MLM KD


Hmm a duk lokacin da tattausan lafazinki  ya tunkari ƙofar zuciyata da zummar isar da saƙon farin cikin da ke zuciyarki, sai na ji daddaɗan shauƙin da ruhina ya mallaka sanadin kamuwa da  ƙaunarki ya zo tarbar shi a daidai gaɓar gangar jiki da kuma ruhina, haƙiƙa wannan ƙwaƙƙwaran dalilin shi ne mahaɗin ƙwarin gwiwar da ta sa nake ji a jikina ke ta musamman ce domin ba da iya zuciya kaɗai nake ƙaunarki ba, har da jin ki a raina ma.


Uhmm Allah sarki zuciyata haƙiƙa na kan ji tausayin kaina a bisa yadda na ga zuciyata tana rarraba aikin ƙaunarki izuwa sassan jikina, domin tun kafin a je ko'ina har na kai matakin da ba zan iya rayuwa babu ke ba.


Ina da tarin burika a cikin rayuwata amma mallakar zahirin mafarkin sace zuciyar kyakkywar gimbiyata shi ne rubutun da zuciyata ke iya karantawa a koyaushe, kuma shi ne karatun da bakina yake maimaitawa a yanzu haka.


Nauyin furuci ko faɗin cewar ke kyakkyawa ce ba'a iya wuyana kaɗai ya rataya ba, haƙiƙa wannan nauyin ya rataya ne a wuyan duk wanda ya samu nasarar yin tozali da kyakkyawar fuskarki. Bugu da ƙari ma a ce kin bayyana kyakkywan murmushin ki a lokacin.


Indai har zuciyata za ta iya samun farin ciki sanadin gani ko jin haɗaɗɗiyar lallausar muryarki, to mene ne zai hana zuciyata zumuɗin san kasancewa da ke? Ke ce wacce zuciyata ta sahalewa  rayuwa da ita ta har abada.  Saƙo daga naki sarkin soyayyar ki.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku ko masoyan ku da dukkan waɗanda ma ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.