Tuesday 26 September 2017

An hana ni aure saboda zargin luwadi – Adam A Zango

Tura Wannan Zuwa Ga

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A
Zango, ya ce a kullum yana kwana yana tashi da
bakin cikin zargin da wasu suke yi masa na
zama dan luwadi (neman maza).

A wata hira ta musamman da BBC, Zango ya ce
wannan ne ya sa a wani lokaci a baya jarumin ya
dauki Alkur'ani ya rantse cewa bai taba neman
wani namiji da lalata ba.

"Wannan abin yana hana ni barci, kai har ma na
taba zuwa neman aure amma aka hana ni saboda
haka," in ji Zango.

Game da batun cewa dan wasan yana da girman
kai, jarumin ya kare kansa "Idan kana maganar
masoya kana maganar miliyoyin mutane, to ta ya
ya zan gamsar da su?"

Daga nan ya nemi masoyansa su rika yi masa
uzuri domin shi ma mutum ne kamar kowa,
kamar yadda ya ce.

A karshe ya yi magana kan yadda ake cewa 'yan
wasan Hausa "kudi suke nema kawai", inda ya
ce "muna yin fina-finan da za su kawo mana
kudi."

Adam Zango ya kuma tattauna abubuwa da
dama a hirar ciki har da alakarsa da Ali Nuhu da
Nafisa Abdullahi da sauran batutuwa.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: