Tuesday 26 September 2017

Ba a hada aure da yin fim – Maryam Yahya

Tura Wannan Zuwa

Tauraruwar matashiyar jaruma Maryam Yahya,
mai shekara 20, ta fara haskawa ne a cikin fim
dinta na farko wato Mansoor.

A wata hira da Yusuf Ibrahim Yakasai, ta shaida
masa ta taka rawar babbar jaruma a fim din duk
da cewa shi ne fitowarta ta farko a fina-finan
Kannywood, saboda ta kudurci aniyar taka rawar
da masu shirya fim din suka umarce ta duk da
kasancewarta sabuwar fitowa.
Ta kara cewa ainahi ba ita ce wadda za ta fito a
matsayin jarumar fim din ba tun da fari, ta samu
zama tauraruwar ne saboda rashin zuwan ainahin
jarumar a kan lokaci, kuma daman tana cikin fim
din sai dai fitowa biyu kadai aka shirya za ta yi.

Ta ce ''Ali Nuhu ne ya sanya aka zabo mu biyu a
cikin wadanda za su yi fitowa ta musamman, ya
ba mu rubutaccen labarin fim din muka karanta
Allah cikin ikonsa sai na kasance wadda ta yi
daidai abin da ya bukata, ka ji yadda akai na
zama jarumar fim din Mansoor,'' in ji jaruma
Maryam.

Maryam ta kara da cewa: ''Da fari na dan ji tsoro,
don ita dayar da aka ba mu labarin muka karanta
tare ta ce kawai na je ina ta dari-dari. Ina farawa
sai na ga an fara tafi da ihu kawai sai sarki Ali
ya ce aje a fara aiki.''

Da aka tambaye ta ko yaya ta ji da aka ce ita ce,
za ta zama tauraruwar fim din?
Sai ta kada baki ta ce ''Na ji wani dadi da ba zan
iya fasalta yadda na ji ba, amma kam ina cikin
tsananin farin ciki a wannan lokacin.'' in ji
Maryam.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: