Tuesday 26 September 2017

Hakika Dan Uwa za kayi kuka in ka ka karanta.....

Tura Wannan Zuwa
Sayyada Aisha (RD) ta tambayi manzon Allah
(SAW) akan saukan wannan ayar:
(Ranar da za a canza qasa banda wannan qasar
da sammai).


Tace masa to a wannan ranar(rananr da ba qasa
b sama) ina zamu kasance(yan Adam)? Se
manzon SAW yace ranar zamu kasance akan
SIRADI(Ma'anar kalmar:hanya)
A lokacin da za'a wuce siradi lokacin babu wani
abu babu kuma ko wani guri se guri uku kawai:
JAHANNAM(ALLAH KA KIYAYEMU )
ALJANNAH(ALLAH KA SA DAMU )
SIRADI

Manzon Allah yana cewa :
Wanda ze fara tsallaka siradi ranar ni ne da
al'ummata. Farkon al'ummar da zata fara wuce
siradi shine alummar Annabi MUHAMMAD(SAW)
ALLAH MUN GODE MAKA.

Ma'anar siradi;
Shin wai menene ita wannan siradin????
Itace ranar da babu sama babu qasa ba komai se
wuta da Aljannah.

Sannan kafun ka kai aljannah dole se ka wuce
jahannama don haka za'ayi wani bridge a saman
jahannama wanda ake kiranta"SIRADI"(WATO
HANYA) tana saman jahannama wanda se ka bi
takanta har qarshenta sannan ka isa qofar
aljanna
Alokacin da ka isa kofar Aljannah za ka tarda
manzon Allah SAW a gaban yana tarban yan
Aljannah(Allah ka bamu Ajannarka)

Siffofin siradi:
1 siranta tafi gashin kai siranta
2 tana da kaifi tafi wuqa kaifi
3 tana da matsanaicin duhu kuma a qarqashin ta
jahannama ne baqiqqirin
(Wuceta ma babban azaba ne )
4 kowa zai dauki zunibinsa a bayansa ya goya.
Idan zunubanka suna da nauyi to zata sanya
maka tafiya a slow WA IYAZUBILLAH
idan kuma zunubanka basu da nauyi zaka wuce
da sauri kamar walqiya
5 a kanta akwai manyan karnuka a kasanta kuma
qayoyi ne masu kaifin gaske suna yayyanka
maka qafa
6 zakaji sauti me tsananin qara ga duk wanda
qafarsa ta kufce ya fada a jahannama
(Allah ka kiyayemu)

A lokacin manzon Allah ze kasance a qofar
Aljannah yana kallon duk wanda ya daura kafarsa
akan farkon siradi yana masa addu'a yana cewa:
Ya Rabbi Sallim. Ya Rabbi sallim
MASOYINMU MANZON ALLAH

A ranar ko wani bawa yana ganin mutane a
gabansa wasu suna fadi wasu suna tsira amma
ranar ba ruwan kowa da kowa
Ranar da bawa ze ga babansa,mamansa, amma
ba ruwansa dasu(sbd tsananin ranar ) saboda
a lokacin kowa ta kansa yakeyi. ﻳﻮﻡ ﻻ ﻳﻨﻔﻊ ﻣﺎﻝ ﻭ
ﻻ ﺑﻨﻮﻥ ﺇﻻ ﻣﻦ ﺃﺗﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻘﻠﺐ ﺳﻠﻴﻢ

An ruwaito cewa sayyada Aisha wata rana ta
tuno da ranar Alqiyamah se ta fashe da kuka se
manzon Allah ya tambayeta me sata kuka?? Se
tace na tuno ranar alqiyamah ne shin kuwa a
ranar zamu tuna da iyayenmu?? Ranar masoyi ze
tuna masoyinsa??

Se manzon Allah yace eh se de a wuri uku
kawai: lokacin da ake auna mizani, da lokacin da
za'a bawa kowa littafinsa, da kuma a gurin siradi
Kuyi haquri(inji masoyinmu manzon Allah SAW
) akan fitintinun duniya muyi jihadin
kanmu kuma mu taimaka ma juna sbd mu hadu
aljannah... girmanta yafi sama da qasa...........
Allah ka sanyamu daga cikin masu tsallaka siradi
lafiyaaaa
Bayan wannan duka (ya kai dan Adam me
hankali) kana tunanin akwai wanda ya cancanci
ka yi masa bakin ciki ko hassada ko tsana ka
batar da ayyukanka a banza????

NASIHA(ka bar halitta ga mahaliccinsu)
Ka tambayi kan ka shekarana nawa? nawa ya
ragemun? Shin kana da guarantee zaka rayu
bayan awa daya?
Ko bayan minti daya?
Kai ko bayan second daya nan gaba??

Kar ku manta iblis(la'annanne) yana cewa Allah
na rantse da izzarka da jalalarka se na batar
dasu muddin rayukan su na jikinsu
Allah kuma yana cewa Na rantse da izza ta da
jalala ta se na gafarta musu muddin suna neman
gafara ta (ASTAGFIRULLAH)

Yan uwana mu yawaita istigfari
ALLAH KASA WANNAN TUNATARWA DA NAYI
YA ZAMA SADAKA A GARENI DA IYAYENA DA
YAN UWANA GABA DAYA da duk wanda ya tura
wannan sako ga yan'uwansa da kuma wanda ya
karanta

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user