Tuesday 26 September 2017

Ma'aikaciyar British Airways 'ta ci zarafin' 'yan Nigeria a bidiyo

Tura Wannan Zuwa Ga

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na mallakin
Birtaniya, British Airways, ya kaddamar da wani
bincike kan wani bidiyo da bayyana, inda daya
daga cikin ma'aikatan jiragensu ta yi wasu
kalaman da ake danganta su da na nuna wariyar
launin fata kan 'yan Najeriya.

Ma'aikaciyar dai ta dauki bidiyon kanta ne a
yayin da take kan hanyarta ta zuwa filin jirgi inda
a ranar za ta yi aiki da jirgin da zai tafi Abuja
babban birnin Najeriya daga filin jirgin sama na
Heathrow da ke London.

A wani sako da kamfanin BA ya aikewa BBC ya
ce: "Tun bayan da aka jawo hankalinmu kan
bayyanar bidiyon, muka fara bincike.

"Ba za mu yarda da kalaman da za su bata wa
abokan huldarmu rai ba ko su musguna musu,
don haka za mu dauki matakin da ya dace a ko
yaushe.

Muna sa ran ma'aikatanmu su zama kwararru a
duk lokacin da suke wakiltar British Airways."

Ma'aiakaciyar dai ta dauki bidiyon ne a cikin
motarta, inda daga bisani ya yadu a tsakanin
abokan aikinta, wadanda su kuma suka sanar da
kamfanin halin da ake ciki.

A cikin bidiyon dai matar tana cewa ne, "Yanzu
zan hau jirgin wadannan 'yan Najeriyar da za su
damu mutum da yi min kaza da kaza, ko kuma a
sauya min wajen zama, mazan ma har cewa za
su yi suna son a mayar da su wajen da za su
sake sosai."

Ma'aikaciyar ta kara da cewa: "Duk 'yan Najeriya
za su dinga damunka da ba ni Coca-Cola, ba ni
naman shanu shi na fi so. Me ya sa naman ya
kare?

"Sai ya kasance ba ni da abin cewa sai, 'Yi hakuri
naman ne ya kare.'

Ta kuma ci gaba da cewa: "Wannan dare na
Juma'a ba zai min dadi ba don zan yi tafiya da
mutanen da ba su da aiki sai damun mutum da
tambaye-tambaye ko korafi."

Kafar yada Labarai ta Daily Mail Online wacce
ita ta fara yada wannan labari, ta ce an bai wa
bidiyon suna: 'Ba zan iya da azabar tafiya a
wannan jirgin ba."

Tuni dai wannan al'amari ya jawo ce-ce-ku-ce a
kafafen sada zumunta na zamani a Najeriya, inda
aka dinga mayar da martani ga kamfanin na BA.

Ana kuma danganta kalaman matar da cewa
kalaman nuna wariya ne.
Da yawan 'yan Najeriya da ke tsokaci kan batun
na nuna zallar bacin ransu ne kan abin da matar
ta yi, tare da goranta wa kamfanin na BA cewa
dama can ba su cika mutunta 'yan Najeriya ba.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: