Tuesday 26 September 2017

Kishin kasa ne ya sa na karbi mukamin minista — Okonjo- Iweala

Tura Wannan Zuwa Ga

Tsohuwar ministar kudi ta Nigeria, Dr. Ngozi
Okonjo-Iweala, ta ce kishin kasa na daga cikin
muhimman dalilan da suka sa ta rike mukamin
ministar kudi har sau biyu a kasar.
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana haka ne a
wani shirin Turanci na rediyo da BBC ke
gabatarwa mai suna "The Conversation" .
Tsohuwar ministar ta ce, mahaifinta ya koyar da
ita kishin kasa, dan haka ta yi iya bakin kokarinta
wajen ganin ta bayar da gudunmuwar da ta dace
a lokacin da take rike da mukaman gwamnati.
Dr. Ngozi ta ce, a lokacin da ta rike mukamin
minista a farko, ta yi kokari wajen kawo sauye-
sauye, wanda har ta kai an samu nasarar yafe
wa Najeriya wasu basuka da ake binta.
Tsohuwar ministar ta ce, a lokacin da aka ba ta
mukamin minista na farko, ta yi fargaba, saboda
rike mukamin ministar kudi ba karamin abu ba ne
musamman a kasa kamar Najeriya.
Dr. Ngozi ta ce wa'adinta na farko a kan
mukamin minista shi ya fi ba ta wahala, amma
ko da ta sake dawowa a karo na biyu, ba ta ji
komai ba, saboda ta san abubuwa da dama ke
tattare da mukamin ministar kudin da aka sake
ba ta.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: