Sunday 21 April 2024

Karanta Zafafan Sakonnin Barka Da Sallah Na Zamani Masu Ratsa Sassan Jiki Da Zuciya

Tura Wannan Zuwa Ga

KYAWAWA


Na ga kyawawa amma ban ga tamkar ki ba. Na ga lalle amma ban ga irin naki ba. Sun saka kaya, amma ba su yi musu kyau irin naki ba, ba wai zuzuta ki nake ba, idan na ce da a ce kin bai wa maza fuska a yau, da kuwa na rasa ki. Hmm kyawu sai mai shi. Ado sai gidansa. Barka Da Sallah 'Yammata. Ina son ki!


Saƙonnin Barka Da Sallah
Hoto: Freepik


BURGE


Abin da zan faɗa miki a yau, abu ne wanda da a ce madubi yana magana, zai faɗa miki kafin ni, kin haɗu, ma'ana kin yi matuƙar haɗuwa, duk namijin da kika wuce ta gabansa, koda bai faɗa ba a zahiri kin ji ba, na tabbata dole a zuciyarsa sai ya ce MASHA ALLAH!. Ba maganar mata ake ba, don ko ba a faɗa ba, dole za su yi miki hassadar kyawun da kika yi. An matuƙar burge ni. Barka Da Sallah. Ina son ki!


SAFIYA 


Kyakkyawar safiyar rana ta musamman zuwa ga wacce murmushin ta kaɗai haske ne, da ka iya kore duhun zuciyar namiji ko shi wane ne, ko ba lalle sabon ɗinki ko kwalliya, ɗari bisa ɗari na yi imani sai kin fi kowa haskawa a yau, ba na shakka na saka ko nawa ne kan cewa sai kin fi kowacce mace ɗaukar ido da samun makalla (Masu kallo/Masu Gani). Na yarda da gwanata. Barka da sallah. Ina son ki.


HOTO


Kwanaki talatin, sa'o'i ɗari bakwai da ashirin, mintina dubu arba'in da uku da ɗari biyu, daƙiƙu miliyan biyu da ɗari biyar da dubu casa'in da biyu, na shafe ina kintata yadda kwalliyar ki ta yau za ta kasance, na bijiro da hotunan ki cikin kwalliya daban-daban, amma har zuwa yau ƙwaƙwalwata ta kasa tsai da hoto ɗaya wanda ya dace da irin kyawun da za ki yi a yau. Ina fatan ko ban zamo na farko ba, kada na zamo na ƙarshen da zai ga irin kyawun da kika yi a yau.


KWALLIYA


Kin fasa zuciyata da kwalliyar ki 'Yammata, kin ƙafar da ruwan idanuwana gurin kallon ki, kin hana bakina rufewa da haɗewar ki, kalma ɗaya tak ta rage a kalaman bakina shi ne an burge ni. Kyawun da kika yi a yau 'Yammata ya wuce na ce komai face Allah ya kare min ke daga masu kambun ido. Barka da sallah.


ƊARI


Idan za ki rayu na tsawon shekaru ɗari a duniya, ni kuma zan so na rayu na tsawon shekaru ɗari ba ɗaya, domin ba zan so na rayu a cikin wunin da babu ke a cikin shi ba. Idan ma'anar soyayya shi ne fifita farin cikin wanda kake so fiye da naka farin cikin. To, kuwa har abada 'Yammata farin cikin ki ne a saman nawa farin cikin. Sannan saka ki farin ciki nauyi ne a gare ni, wanda matuƙar ban sauke wannan nauyin ba, har abada ba zan taɓa samun natsuwa a zuciyata ba. Ina son ki.


SOYAYYA


Idan na faɗi a ko'ina ne zan tashi na ci gaba da tafiya, amma daga lokacin da na faɗi a soyayyar ki wataƙil ba zan kuma tashi na tsawon rayuwata, faɗuwa a jarabawa ko a neman aiki da kasuwanci ba sa tayar min da hankali. Babban taraddadin zuciyata shi ne zamo wa mara nasara a soyayyar ki, fatana a kodayaushe na yi nasara a zuciyar ki, burina a kullum na mallake ki a matsayin mata a gare ni. Idan wannan burin nawa ya cika, har abada ba na da wata sauran damuwa. Ina son ki 'Yammata.


FUSKA


Zama a kusa da ke ko babu aikin komai shi ne kusan komai a gare ni, aikin kallon kyakkyawar fuskar ki kaɗai ya fiye min duk wani aiki da zan yi, domin kuwa 'yammata bambancin aikin kallon ki da sauran ayyuka shi ne sauran ayyuka gajiyar da ni za su yi. Aikin kallon ki kuma kore min gajiyar zai yi, don haka nake ganin shafe tsawon rayuwata ina aikin kallon ki ba zai taɓa gajiyar da ni ko ya sa min damuwa ba. Ina son ki.


TARIHI


A gurina duk ranaku ɗaya ne, idan ban da ranar da na fara ɗora idanuwana akan kyakkyawar ki, wannan ranar kam daban ce, tana da rubutaccen tarihi a zuciyata, tana da keɓantaccen muhimmanci a rayuwata, kuma tana da haske na musamman a raina, 'Yammata samun ki babbar ni'ima ce a gare ni, domin kuwa da shigowar ki rayuwata kika sauya komai a tare ni, kika ba ni farin ciki a madadin damuwa, kika ba ni haske a madadin duhu. Ina son ki.


TAMBAYA


Ke ce ranar da ke haska wunina, iskar da ke kaɗawa a sararin duniyata, numfashin da yake rayar da gangar jikina, haka ma wacce sunan ta ne rubuce a tarihin rayuwata, 'Yammata idan za ki tambaye ni ina son ki kuwa? Amsa ta a kullum za ta kasance sosai ma kuwa. Idan za ki tambaye ni zan iya barin ki a rayuwata? Amsa ta ga wannan tambayar shi ne koda wasa. Idan kuwa tambayar ki ta kasance wacce mace ce na fi so a rayuwata? Ko ƙarisa tambayar ba za ki yi ba, zan tare ki da amsar cewa ke ce.


FUSHI


Duk tsananin hasken da rana take da shi, hasken ta bai taɓa haskawa cikin zuciyata ba, amma shigowar ki rayuwata, sai ga shi hasken ki ya haske zuciyata fiye da yadda rana ke haska duniya, da haska zuciyata da kika yi, a yau kin zamo nuril ƙalbi (Hasken zuciya) kuma nuril hayati (Hasken rayuwa), 'Yammata zuwan ki cikin rayuwata ya kore dukkan duhun da na kasance a ciki, ke alkhairi ce a gare ni 'Yammata, ba zan taɓa rabuwa da ke ba, ba zan taɓa iya fushi da ke ba. Ina son ki.


KYAUTA 


Ni kawai roƙar Allah na yi ya ba ni azurfa, gwanin kyautar kuma sai ya ba ni zinare, ban taɓa sa ma kaina dogon burin samun kyakkyawar mace tamkar ki ba a rayuwata, amma sai ga Ubangiji ya ba ni ke 'Yammata, macen da ta fi kuma ta zarce sauran mata, wacce a matsayi sai dai a kira ta da gimbiyar mata, a ƙananun shekaru autar mata, a ilimi da sanin ya kamata kuma dole a kira ta da sayyadar mata, a zubi tsari da kyawun surar ki dole a kira ki sarauniyar mata ko maƙiyin ki ne ya ce ba ya son ki, bakinsa ne yake faɗar abin da ba shi ba ne a zuciyarsa ba. Ina son ki. 


DUNIYA


Zan saka ki farin ciki yayin da kika shiga damuwa, zan saka ki dariya yayin da wani ya ɓata ran ki, zan zamo bango yayin da kike buƙatar dafawa, zan zamo ƙwarin gwiwar ki yayin da kike da wani buri da kike son cimma wa, 'Yammata ko na faɗa ko kar na faɗa abu ne da kowa zai iya fahimta a tare da ni cewa na kamu da matuƙar son ki. Idan na kira ki da jannati, wannan don zamowar ki Aljannar Duniyata ce. Idan na kira ki da hayati, wannan don kin kasance rayuwata ce. Ina matuƙar son ki Jannati. Ina son ki!


Sanusi Kabir ne ya gabatar da su, wakilin mu ya fitar da su a rubuce, ga dukkan wanda yake son ya saurare su a ainihin yadda suke, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user