Sunday 21 April 2024

Hikimomin Rayuwa 5 Ga Masu Son Cimma Nasara

Tura Wannan Zuwa

1. SAURARON GAZAWARMU – KARƁAR TSOKACI: Wato mafi yawanci muna da matsala wajen sauraron matsalolin mu, ko a ci gyaran mu. Hikimar sauraron tsokaci na ɗaukar lokaci wajen koyo da ƙwarewa, kuma yadda ake yi shi ne, ka kau da duk wani abu da kake ji a cikin zuciyarka, ka mayar da hankali akan bayanan da ake ba ka. Wani gyaran yana da amfani, wani kuma ba shi da shi. Ka yi amfani da ƙwaƙwalwarka wajen tantancewa, ba zuciyarka ba.


Hikimomin Rayuwa
Hoto: Unsplash


MarubuciBello Galadanchi


2. MIƘEWA BAYAN FAƊUWA: Kar ka karaya. Ka miƙe, ka watsake, sannan ka yi amfani da darrusan da ka koya domin ƙara wa kanka ƙarfin zuciya da taurin rai domin shiryawa gaba. Wannan hikima tana da wahala, amma sinadari ne mai muhimmanci idan har kana so ka samu ci-gaba a rayuwa.


3. BADA HAKURI: Dole sai ya fito daga zuci, kuma ka bayyana yadda za ka yi ƙoƙarin kiyayewa gaba. Kar ka bada haƙuri kamar haka:


"Ka yi hakuri saboda na ɓata maka rai. Hanzari nake shiyasa na yi wannan kuskure."


Ka gani anan, haƙurin ya mayar da hankali ne akan yadda wanda aka ɓatawa rai yake ji, ba abin da ka yi ba da yadda za ka kiyaye. A guji bada irin wannan hakuri.


Ga misali mai kyau:


"Ka yi hakuri saboda laifin da na yi. Na makara ne wajen tashi daga bacci shiyasa ban iso da wuri ba. Nan gaba, zan kwanta da wuri, sannan zan yi amfani da wayata wajen tuna min da lokacin da ya kamata na tashi."


4. GODIYA: Ka tantance mutanen da ke ba ka goyon baya da faranta maka rai, sannan ka bayyana musu yadda kake ji. Ka tabbatar sun san cewa suna da matuƙar muhimmanci a rayuwarka, kuma kana matuƙar darajanta su. Babu wanda zai iya rayuwa shi kaɗai a duniyar nan, saboda haka ka zama mai mutunci da zumunci.


5. FAHIMTAR ABUBUWAN DA SUKA FI MUHIMMANCI: Ka tabbatar ka yi amfani da lokacinka da kadarorinka akan batutuwan da suka fi muhimmanci. 


Mutane da yawa na cakuɗa abubuwa da yawa a rayuwarsu ta yau da kullum saboda ba su san ko mene ne ya fi muhimmanci ba.


Ka rubuta duk abubuwan da kake aiki akai, sannan ka jera su daga wanda ya fi muhimmanci a farko, zuwa wanda ba shi da tasiri sosai a ƙarshe. Ka rubuta lokutan da za ka aiwatar da su, sannan ka fara aiki. 


Allah Ya shige mana gaba.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user