Wednesday 20 September 2017

BA NA NEMAN MIJIN AURE- ZEE ZEE

Tura Wannan Zuwa Ga

Fitacciyar ’yar fim din Hausar
nan Ummi Ibrahim wacce aka
fi sani da Ummi Zee-Zee, ta
musanta batun da wasu
kafafen watsa labarai suka
buga cewa tana neman mijin
aure.

Ummi ta ce a matsayinta na
fitacciyar jaruma, ta fi karfin
ta fito kafafen watsa labarai
tana neman mijin da zai aure
ta, baya ga dimbin masoyan
da ta ce Allah Ya ba ta,
wadanda kuma ta bayyana
cewa a shirye suke a kowane
lokaci su aure ta.

A cewarta, ba ta ji dadin
maganar ba, haka kuma cin
fuska ne kai-tsaye a
danganta ta da wannan batu.

“A gaskiya ban ji dadin
wannan magana ba. Ta yaya
ma za a ce ina neman miji?

Idan aure nake so ina da
mazan da a shirye suke su
fito su aure ni, don haka ba
wani batun neman ma’auri da
nake yi,” inji ta.

Aminiya ta gano cewa an
dauki tsawon lokaci ba a
ganin ’yar fim Ummi Zee-Zee
a fina-finan Hausa, saboda
tafiya hutun da ta yi kamar
yadda jarumar ta shaida wa
jaridar.

Jarumar dai ta bayyana cewa
a yanzu haka ma tana nan
tana shirye-shiryen dawowa
harkar fim gadan-gadan, inda
take shirya wasu manyan
fina-finai. “Ina yi wa

masoyana albishir cewa su sa
ido a hanya, domin ina nan
ina shirye-shiryen dawowa
harkar fim din Hausa
tsundum. Ina nan zan dawo
da karfina, domin zan shirya
wasu manyan fina-finai insha
Allahu,” inji ta.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: