Wednesday 20 September 2017

Ba ni da hannu a daukar nauyin IPOB — Jonathan

Tura Wannan Zuwa

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan,
ya ce ikirarin da ministan yada labaran kasar,
Lai Mohammed, ya yi cewar 'yan hamayya ne ke
daukar nauyin kungiyar masu fafatukar kafa
kasar Biafra ta IPOB ya nuna cewar har yanzu
gwamnatin Buhari na ci gaba da yada farfaganda
maimakon mayar da hankali kan aiki.

A wata sanarwar da Reno Omokri, mataimaki na
musamman kan shafukan sadarwar zamani ga
Shugaba Goodluck Jonathan, ya wallafa a shafin
Facebook na tsohon shugaban kasar, cewa idan
gwamnatin Najeriya ta san 'yan hamayyar da ke
daukar nauyin 'yan IPOB, ta kama su tare da
gurfanar da su gaban kotu.

Mista Jonathan ya ce bai dace a yi amfani da
soji wajen dakile laifuka a cikin gida ba, domin
an ba su horarwar yakar abokan gabar kasa da
ke waje ne.

Ya ce maimakon soji, 'yan sanda ne ya kamata a
yi amfani da su wajen kwantar da tarzomar cikin
kasa.

Tsohon shugaban Najeriyar ya kara da cewar,
idan sojoji suka fara yi wa fararen hula barazana,
to maimakon a kwantar da tarzoma sai hakan ya
zama barazana ga mutane.

A shekarar 2015 ne Mista Goodluck Jonathan ya
mika mulki ga Shugaba Buhari bayan ya sha kaye
a zaben shugaban kasa da aka gudanar a
shekarar.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: