Wednesday 20 September 2017

Idan Ban Iya Turanci ba hakan baya nufin Ni Jahili bane-Adam A. Zango

Tura Wannan Zuwa

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa,
Adam A. Zango, ya ce babban burinsa
shi ne ya kware wajen magana da
harshen Turanci.

Zango, wanda aka haifa a garin Zangon
Kataf na jihar Kaduna, ya yi karatun
sakandare a birnin Jos na jihar Plateau
ne.

Jarumin ya ce zai bar sana’arsa nan da
dan wani lokaci domin ya je ya ci gaba
da karatun boko.
A yanzu haka dai jarumin ya dauki
malamin da yake ba shi darussa a gida,
kafin ya koma makaranta don ci gaba
da karatun.

“Yanzu haka na kammala sakandare
kuma ina son ci gaba da karatu, ko da
zuwa matakin difiloma ne. Abin da
nake so shi ne na iya Turanci sosai,” in
ji Adam Zango a wata hira da ya yi da
BBC.

Sai dai wani abu da Adam ya ce yana ci
masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu
‘yan boko suke masa kallon jahili duk
kuwa da cewa “na yi karatun bokon
sannan kuma ina da ilimin addini.”

Batun ilimin boko ne dai ya taba sa
Adam ya wallafa wani habaici a
shafinsa na Instagram da bai yi wa
wasu ‘yan boko dadi ba, al’amarin da
har ya sanya jarumin yin da-na-sani.

“Yanzu haka na kammala sakandare
kuma ina son ci gaba da karatu, ko da
zuwa matakin difiloma ne. Abin da
nake so shi ne na iya Turanci sosai,” in
ji Adam Zango a wata hira da ya yi da
BBC.

Sai dai wani abu da Adam ya ce yana ci
masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu
‘yan boko suke masa kallon jahili duk
kuwa da cewa “na yi karatun bokon
sannan kuma ina da ilimin addini.”

Batun ilimin boko ne dai ya taba sa
Adam ya wallafa wani habaici a
shafinsa na Instagram da bai yi wa
wasu ‘yan boko dadi ba, al’amarin da
har ya sanya jarumin yin da-na-sani.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: