Wednesday 20 September 2017

Shin ko Kasan Abubuwa Biyar da su faru a Kannywood????

Tura Wannan Zuwa

1. Auren jinsi
Wani abu da ya jan hankalin jamaa
sosai kuma ya tayar da jijiyar wuya shi
ne zargi hada auren jinsi da aka yi wa
wasu taurarin Kannywood hudu da yi a
birnin Kano a watan Afrilun shekarar
2007.

Lamarin da ya sa suka shiga buya,
bayan
hukumar shari’a ta Hizba ta samu
labarin sannan ta shiga nemansu.
Ko da yake a wata hira daakayi da
Aunty Maiduguri wadda aka zarga da
hada auren ta musanta zargin.

2. Fim din batsa ko Blue Film
‘Yan Kannywood sun samu kansu a
tsaka mai
wuya a watan Agustan shekarar ta
2007, inda
aka zargi Maryam Usman Hiyana da
Saurayinta Usman Bobo da yin fim din
batsa.

Fim din da aka yita yadawa kuma ya
janyo
matukar suka ga masu harkar fina-
finan.
Fim din batsan ne kuma ya kawo
karshen fitowar Hiyana a fina-finan
Hausa bayan an kore ta.

3. Zargin luwadi
A watan Agustan 2016 ne kuma zargin
luwadi ya dabaibayi masana’antar.
Lamarin da ya kai har fitaccen jarumin
nan kuma mawaki, Adam A Zango,
rantsuwa da alkur’ani mai tsarki yana
kare kansa. Batun ya taso ne bayan da
aka zargi wasu daga
cikin masu harkar fimdin da cewa ‘yan
luwadi ne.

Sai dai a wannan karon babu wani da
aka
fayyace sunansa.

4. Gina alkaryar fim
Batun gina alkaryar fim a jihar Kano
wanda
gwamnatin tarayyar ta so gudabarwa
ya tayar da jijiyoyin wuya a baya a
watan Julin bana.

Malaman addini da jama’a ne suka
nuna adawa da shirin, suna masu cewa
zai daurewa badala da shashanci gindi
a jihar.
Sun zargi ‘yan fim da cewa mutane
marasa
kamala da ke yada batsa.

Sai dai masu shirya fim din sun ce ba
haka
lamarin ya ke ba, kuma mummunar
fahimta ake
yi musu.

5. Rahama Sadau ta rungumi Classiq
Batun rungumar mawakin nan, Classiq
da
Rahama Sadau ta yi shi ne abu na baya-
bayan nan da ke jan hankali masu bin
al’amuran Kannywood da ma jama’ar
gari.

Yayin da wasu ke sukarta kuma
kungiyar shirya fina-finan Hausa ta
kore ta, Rahama ta nemi gafara tare da
kokarin fahimtar da mutane cewa duk
abin da ta yi a wakar aikinta ne ya
bukaci haka ba son rai ba.
Kungiyar ta ce ‘yar wasan ta yi karan-
tsaye ga
ka’idojin kyawawan dabi’un da
Kannywood ta
ginu a kansu, lamarin da ta ce
shugabannin
harkar ba za su lamunce da shi ba.

Sai dai wasu na korafin cewa akwai
wasu ‘yan
wasan da a cewarsu suka yi abin da ya
fi na
Rahama, kuma ba a dauki mataki a
kansu ba.

Masu korafin na ganin an kawar da kai
ga abin da taurarin fina-finai kamar su
Ali Nuhu da Sani
Danja da kuma Adam A Zango ke yi a
wasu fina-
finan ko wakoki.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Real Lawal Usman

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: